May 27, 2016 13:55 UTC

A shirin na yau zamu leka Najeriya, inda kungiyar kwadago ta NLC ta janye yajin aikin gama garin da ta kira a ranar Laraba data gabata; zamu leka Jamhuriyar Niger inda wasu tsageru da ake kautata zaton ‘yan boko haram ne suka kashe mutane 20 a kauyen Yebi dake kusa da Garin Bosso a gabashin kasar, sanan kuma zaku ji cewa a wannan mako ne kasar Kamaru ta gudanar da bikin kasa karo na 44

To bari mu dauko shirin kan batun siyasa inda Jam’iyyar PDP a Najeriya ta kori Shugabanta na kasa Ali Modu Sheriff.

Inda ta nada tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi a matsayin shugaban rikon kwarya.

Jam’iyyar ta kuma nada tsohon gwamann Anambra Peter Obi a matsayin mukadashin sakataren Jam’iyyar.

A cewar Jam’iyyar ta dau wannan matakin ne domin shawon kan rigingimun da suka mamaye ta, inda sabbin shugabannin data nada yanzu zasu ja ragamar jam’iyyar zuwa tsawon watanni Uku nan gaba.

…………………………..

A Najeriya kuma kungiyar kwadigo ta kasar NLC ta janya yajin aikin gama gari da ta kira a ranar Laraba data gabata, domin kalubalantar matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur

………………………….

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da daya daga cikin ‘yan matan sakandaren garin Chibok da aka ceto daga hannu mayakan Boko Haram Amina Ali Nkike.

Amina da aka ceto da taimakon ‘yan kato da gora a ranar talatar data gabata, ta isa fadar shugaban kasa da mahaifiyarta Binta da kuma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da wasu jami’an gwamnati da suka hada da babban hafsan tsaron kasar.

Gano Amina yanzu ya sake baiwa gwamnati kasar kwarin gwiwa a kokarin da ake wajen ceto ‘yan mata da akayi awan gaba dasu sama da shekaru biyu.

………………………

A Jamhuriya nijar,  bayanai daga mazauna yankin Bosso a gabashin kasar ke cewa rayukan mutane akalla 20 ne suka salwanta sakamakon wani farmaka da wadansu da ake kautata zaton tsagerun boko Haram suka kai a kauyen a garin Yebi na yankin Bosso a cikin daren ranar Alhamis da ta gabata.

mazauna yankin sun shaidawa wakilim mu a Zinder Musa Mal. Suley cewa an samu mutane akalla 20 da suka mutu, saidai a wata sanarwa data fitar gwamnatin kasar ta ce mutane shida ne suka rasu. 

.....................

To har dai muna Nijar din, amma wannan karo kan matsalar bakin haure Afirka, inda ake ci gaba da samun bakin hauren dake rasa kasar da zumar isa kasashen larabawa inda daga cen su kwarari kasashen Turai.

Matsalar na dada kamari inda yanzu harda ‘ya’ya mata dake shiga wannan tafiye-tafiye À dai dai lokacinda hukumomin kasar suka ce suna bukatar tallafi don dakile wannan matsala.

 wakilin mu Umaru Sani ya tattauna da ma'aikatan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta mdd wato OIM, inda suka bayyana masa ainahin yadda matsalar ta ke a yanzu.

…………………….

A kasar Kenya kungiyoyin kasa da kasa ne ke ci gaba da nuna Damuwa kan yunkurin hukumomin kasar Kenya Na Rufe Sansanin "Yan Gudun Hijira

Yunkurin rufe sansanin ‘yan gudun hijira wanda wanda shine mafi girma a duniya na shan suka yanzu haka daga kungiyoyi daban-daban na duniya.

Sansanin na Dadaab dake Kenya dake kan iyaka da kasar Somalia na da ‘yan gudun hijira da yawan su ya kai 350,000 da suka hada dana kasar Somalia, mai fama da tashe-tashen hankula

A farkon wannan wata ne dai Gwamnatin Kenya ta ce zata rufe sansanin saboda fargaban tsaro.

 …………………………..

A Kamaru, a wannan mako ne kasar ta gudanar da bikin da ta zama jamhuriya karo na 44.

Dakarun Nijar da baki daga kasashen makofta irin Najeriya na daga cikin mahalarta taron na bana, kamar yadda wakilin mu Wada Alhaji ya tattauna da wasu daga cikin su a rahoto daya aiko muna..



Tags