Misdakin Ababen Bauta Koma Bayan Allah
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mu yi bayyani kan siffofin Anida'a wato wadanda ake bautawa koma bayan Allah, tambayarmu ta Yau ita ce shin Alkur'ani mai tsarki ya Ambato misdakin ababen bautar da ake bautawa koma bayan Allah da ya hanemu mu bauta masa? , amma kafin nan bari mu saurari wannan.
**************************Musuc******************************
Masu Saurare, wannan tambaya, mun amsa makamanciyar ta a shirin da ya gabata, kamar yadda Ayoyi na 21,22,165 zuwa 167 na cikin suratu Bakara suka bayyana mana siffofin abinda ake bautawa koma bayan Allah da aka hanemu da bautawa, inda wadannan Ayoyi suka bayyana cewa, abin bauta barkatai koma bayan su makiyan Allah madaukakin sarki ne da babu shakka za su shiga wuta tare da mabiyansu, masu yi musu bauta, kuma A ranar Alkiyama yayin da suka ga Azaba mai radadi za su yiwa wadanda suke bauta musu tawaye.
Masu saurare, batar da Mutane tare da nisantar da su daga hanyar Allah madaidaiciya na tauhidi ko kuma kadaita Allah ita ce siffar Abin bauta barkatai koma bayan Allah, sannan kuma su jefa masu bin su da magoya bayansu cikin bata ta hanyar kawata musu hanyoyin bata barkatai da suka sabawa kyakkyawar fitira. A cikin suratu An'ami Aya ta 137 Allah Tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kamar haka kuma abokan tarayyar tasu suka kawata wa yawan mushrikai kasha 'ya'yansu don su hallakar da su , don kuma su rikitar musu da addininsu, da kuwa Allah ya so to da bas u aikata haka ba.to sai ka bar su da abin da suke kagewa),Masu saurare, wannan Aya mai albarka na ishara kan yadda wadancan abin bauta barkatai koma bayan Allah suke kawata mushrikai mafi munanan aiyuka, kamar kisan kai, suna siffanta musu shi a matsayin kyakkyawan aiki da ake samun kusancin Allah madaukakin sarki da shi, suna sanya musu mugan kaya domin bata addininsu, kuma wannan shi ne abinda sarakunan Bani Umaiyya da kuma malimansu masu basu munanan fatawa wajen batar da magoya bayansu, kamar yadda suka kawata mata magoya mumunan aiki har suka kashe Imam Husain (a.s) shugaban gidan Aljanna da ma sauren zuriyar Annabi Muhamadu (s.a.w) domin biyayya ga Yazid bn Ma'awuya a matsayin khalifan kuma daya daga cikin makusantan Ubangiji. Hakika Shekh Saduk yardar A..ta tabbata a gareshi cikin litattafansa Alkhisan da Al-amaly ya ruwaito hadisi Shugabanmu Imam Zainu Abidin (a.s) ya ce:(babu wata rana kamar ranar Imam Husain yayin da wasu Mazaje dubu 30 suka abkamasa kuma suna tunanin cewa su daga cikin wannan Al'umma ce wato suna tunanin cewa su musulmi ne, ko wane daga cikinsu yana tunanin ya na kusanci da Allah madaukakin sarki ne da jininsa,(a.s) ayin da shi kuma yake tunatar da su, amma wa'azin bai amfane su ba har saida suka kashe shi, cikin zalinci da kiyayya).Masu saurare bayan wannan misdaki, cikin suratu Ibrahimu daga Aya ta 28 zuwa ta 30, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ba ka ga wadanda suka musanya ni'imar Allah da kafirci ba, suka kuma jefa mutanensu gidan hallaka* (watau) jahannama, za su shiga ta, makoma kuma ta munana*suka kuma sanya wa Allah abokan tarayya don su batar (da mutane) daga hanyarsa.ka ce (da su) "ku ji dadi (kadan a duniya) sai dai hakika makomarku wuta ce) dangane da fada tsakanin abin bauta barkatai koma bayan Allah da mabiyansu a ranar Alkiyama, Allah tabaraka wa ta ala cikin suratu Sabi'I Aya ta 33 ya ce:(Raunanan kuma suka ce da manyan Ba haka ba ne, makircin Dare da na rana ne yayin da kuke umartar mu da mu kafirce wa Allah, mu kuma sanya masa abokan tarayya, "Suka kuma bayyana nadama lokacin da suka ga azaba, kuma muka sanya kukumi a wuyan wadanda suka kafirta, ba kuwa za a saka musu da komai ba sai irin abin da suka kasance suna aikatawa) a cikin Suratu Zumar Aya ta 8 Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan kuma wata cuta ta sami mutum sai ya roki Ubangijinsa yana mai komawa gare shi, sannan idan Ya bashi wata Ni'ima daga gare shi, sai ya manta abin da ya kasance yana rokon Sa a da, ya kuma sanya abokan tarayya ga Allah don ya batar (da Mutane) daga hanyarsa (Allah) Ka ce "ka ji dadi dan kadan da kafircinka, hakika kai kam kana cikin 'yan wuta) a cikin suratu fussilat Aya ta 29 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(wadanda kuma suka kafirta suka ce: Ya Ubangijinmu, ka nuna mana Wadanda suka batar da mu na daga Aljanu da mutane, mu sanya su a karkashin dugaduganmu don su zamanto a kasan kasa).
********************************Musuc**************************
Masu saurare wadannan ayoyi masu girma sun bayyana mana misdakin abin bauta barkatai koma bayan Allah da aka hane mu, mu yi musu biyayya ko kuma mu bauta musu domin sune shugabanin bata da suke karkatar da Addinin gaskiya suke kuma jefa mutane cikin kafirci, suna kuma sanyawa ana yiwa Allah girman kai a kan ni'imar da ya yi musu wanda hakan shi zai yi musu jagora zuwa gidan wuta. Kamar yadda Fir'auna ya yi ga mutanasa, wannan shi ne abinda Hadisai suka tabbatar a riwayar da aka ruwaito cikin tafsirin Ayoyin da suka gabata da makamantansu, a cikin Tafsiru Kanzul Daka'ik, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake kwatamta tabbacin Aya ta 8 cikin suratu Zumar a kan daya daga shugabanin bata da ake kira Abi Fusail wanda yake umartar mutane ba tare da hakki na Allah ko na ma'aikinsa ba. A cikin wani hadisi na daban kuma yayin da yake fassarar Aya ta 29 cikin suratu fussilat da ta gabata, Imam (a.s) ya ce (duk wanda ya yi shirka da Imami daga Imaman iyalan gidan Annabta Hakika ya yi shirka ga Annabi ne, kuma duk wanda ya yi shirka ga Annabi, hakika ya yi shirka da Allah).a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s), yayin da yake bayyani kan misdakin Ayoyin da suka gabata na suratu Bakara wadanda suke bayyani kan wadanda suke son wasu abin bauta barkatai koma bayan Allah, Imam (a.s) ya ce:(Wallahi su ne masoya wane da wane sun rike su shugabani koma bayan Limamin da Allah madaukakin sarki ya sanya shi ga Mutane Shugaba, wadannan wallahi sune sugabanin Bata da mabiyansu). Masu Saurare, hakan na tabbatar mana da cewa Shugabanin Bata da wadanda suka zauna a kujerun Shugabanin gaskiya da Allah madaukakin sarki ya zabe su a tsahon tarihi, sune misdakin da tabbashin kishiyoyin Ubangiji wadanda suke batar da Mutane suna kuma toshe hanyar isa zuwa ga madaidaiciyar hanya.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.