Bautar Allah a bangare Bauta a akidance da kuma a aikace
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce minene ma'anar Bautar Allah a bangare Bauta a akidance da kuma a aikace? kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
**************************Musuc*****************************
Masu sausare, idan muka yi nazari a Ayoyin Alkur'ani mai girma da kuma Hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma na iyalan gidansa tsarkaka za mu ga cewa sun bayyana mana ma'anar kadaita Allah wajen Bauta, Abangaren akida zai kasance ta hanyar Imani da cewa shi Allah madaukakin sarki shi ne Ubangijin komai kuma shine mai tsara Al'amuran dukkanin Halittu, a kan wannan hanuwansa a bude suke ma'ana kudurarsa ta watsu ga kowa ba kamar yadda Yahudu suke bayyanawa ba na cewa ya halicci halittu kuma ya bar kowa ya iya da kansa, abinda kuma ake nufi da tauhidin Allah na Bauta a aikace shi ne kasancewar mumuni ya koma ga Allah madaukakin sarki a dukkanin Al'amuransa, ya kuma tafiyar da su kamar yadda Allah madaukakin sarki ya umarce shi, ta hanayar amfani da kuma daukan sakon sa daga wajen masu isar da shi da kuma khalifofinsa da masu shiryar da su da umarnin Allah tabaraka wa ta'ala. Misalin hakan a cikin Suratu An'ami Aya ta 106, Allah subhanahu wa ta'ala ya ce:( Ka bi abin da aka yi maka wahayi daga Ubangijinka, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi,ka kuma kau da kai daga mushrikai) har ila yau cikin wannan Surat mai albarka Aya ta 71 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ka ce (da su) Yanzu kun bauta wa (wata halitta )banda Allah, abin da ba zai amfane mu ba, kuma zai cuce mu ba, mu koma gidan jiya bayan kuwa ga shi Allah ya shirye mu, (mu zame) kamar wanda shaidanu suka batar da shi yana ta dimuwa a bayan kasa ga shi da wasu abokai da suke kiran sa zuwa ga shiriya (suna cewa ka taho nan? Ka ce hakika shiriyar Allah fa ita ce Shiriya kuma an umarce mu cewa mu mika wuya ga Ubangijin Talikai) Kazalika idan muka yi nazari cikin Ayoyi na 161 zuwa na 164 cikin wannan surat za mu fahinci cewa Allah madaukakin sarki ya bayyana mana dukkanin bangarorin tauhidin, a bangaren I'itikadi shine ta hanyar imanin cewa Allah shine mai tsara dukkanin al'amuran Bayi baki daya kuma tsarin sa shine mafi kamala, kadaita Allah a bangare bauta a aikace shine riko da shiriya Ubangiji.Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce (da su):' Hakika ni Ubangijina ya shiryar da ni zuwa ga hanya madaidaiciya,Addini madaidaici,hanyar Ibrahimu mikekkiya kuma bai kasance daga mushrikai ba.*Ka ce (da su): Hakika Sallata da ibadata da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin Talikai: *Ba shi da abokin tarayya.Da wannan aka Umarce ni, kuma ni ne farkon mai mika wuya (a wannan al'amurar). *Ka ce (da su):"Yanzu wanin Allah zan rika Ubangiji, alhali kuwa Shi ne Ubangiji kowane abu? Kuma kowane rai ba ya janyo wa kowa sai kansa, wani rai kuma bay a daukar laifin wani, sannan kuma wurin Ubangijinku ne makomarku, sai ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna sabani game da shi) surata An'ami daga Aya ta 161 zuwa ta 164. Kamar yadda wadannan Ayoyi suka bayyana Allah madaukakin sarki shi kadai ne da amfani ko tsutuwa ke hanunsa kuma shine mahalicin Hallitu, masanin abin da yake maslaha a gare su, domin haka ne ma kadaita shi a bangaren Bauta shine tafiya da kan hanya madaidaiciya, domin shine mai ceto ko kuma kubutarwa daga duk wani nau'I na cutuwa kuma shi ne mai isar da dukkanin nau'I na amfani da alkhairi, a cikin Suratu A'arafi Aya ta 54, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika Ubangijinku (shi ne)Allah wanda ya halicci sammai da kassai cikin (gwargwadon) kwana shida, sannan kuma ya daidaita a kan Al'arshi, dare yana rufe(hasken) yini (kamar yadda hasken yini yake bice duhun dare) kowanne yana bin dan'uwansa a gurguje,rana da Wata da kuma taurari masu bin umarninsa ne.Hakika halitta da sarrafa ta nasa ne,Allah Ubangijin talikai alhairansa suna da yawa).
**********************Musuc*************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Aya ta 16 cikin suratu Ra'adi, inda Allah madaukakin sarki ya ce:(K ace (da su):" Wane ne Ubangijin Sammai da Kassai?" ka ce: Allah ne" ka ce (da su):" Amma yaya kuka riki wasu iyayen giji ba shi ba su zama masoya, ba ma mallakar wani amfani ko cuta ga kansu?" Ka ce : Shin makaho da mai gani za su yi daidai, ko kuwa shin duhu da haske za su yi daidai? Ko sun sanya wa Allah wasu abokan tarayya ne wadanda suka yi halitta kamar halittarsa, sai halittun suka yi kama da juna a gare su?" ka ce: Allah ne Mahaliccin komai, kuma shi ne makadaici mai rinjaye), Masu saurare Hakika kadaita Allah madaukakin sarki a bangare bauta, a akidance ko a aikace shi ne yake samar wa zuciyar mutum nutsuwa da konciyar hankali a wajen komawa ga Ubangiji shi kadai a dukkanin Al'amura,son rai na abin bauta barkatai na shaidanu daga cikin mutane da Aljani ba zai shi narara ba wajen farautarsu na kiransu zuwa biyar abinda su ke so wanda kuma ya sabawa fitira mai kyau. Kamar yadda tauhidin Allah tsarkakekke shi ne yak e karawa mutum kuzari ya samu kyakkyawan sakamako na bin kyakkyawar hanya wacce za ta sanya ya samu dukkanin alkhairai da albarkatu gami da rabauta na Duniya da Lahira, Ma'anar kadaita Allah a bangaren Bauta, shine riko da rukunan Ubangiji mai karfi da kuma kokarin samun hulda da Ubangiji a bangaren Bauta. Wannan shi ne abinda Allah madaukakin sarki ya fadakar da su a cikin Ayoyi na 30 da 31cikin Suratu Hajji, inda yake cewa:(Wannan kuwa (umarni ne daga Allah) duk wanda ya girmama abubuwan da Allah ya hana (a hajji) to shi ya fi masa alheri a wurin Ubangijin sa. An kuma halatta muku dabbobin ni'ima,in ban da wadanda aka karanta muku (haramcinsu).To sai ku nesanci Kazanta ta bauta wa gumaka, kuma ku nesanci fadar shaidar Zur *kuma masu mika wuya ga Allah, ba masu tarayya da shi ba.Wanda kuwa duk ya yi tarayya da Allah, to kamar ya fado ne daga Sama, sai tsutsaye suka fauce shi (suka yanayana shi) ko kuma iska ta jefa shi cikin wani wuri mai zurfi (ta rugurguza shi).
Masu Saurare wadannan bayyanai, tambayar da za ta biyo baya ita ce hanyoyin tsira daga shirka a bangaren kadaita shi a bauta, wannan shi ne abinda shirin mu nag aba zai amsa da yardar Allah madaukakin sarki.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.