Jun 28, 2016 12:20 UTC

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tanbayarmu ta yau ita ce ta ya ya za mu tsira daga bautar wanin Allah ko kuma mu ce shirka a bangaren Bauta? Kafin amsa wannan tambayi bari mu saurari wannan.

**********************Musuc********************************

Masu saurare kamar yadda shirin ya saba ya kan komawa ga Nassosi na  haskaka guda biyu, hasken shiriyar Ubangiji da kuma abin dogoron Shugaban Mursalai cikin Al'umarsa Muhamad tsitra da amincin Allah su tabbata a gareshi wato Alkur'ani mai tsarki da kuma haske na biyu shine shiriyar Iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a garesu baki dayansu.Masu saurare sakka babu tsira daga bautar wanin Allah ko shirka a bangaren a akidance ya fi sauki da na aikace, domin idan mutum ya aminci a cikin zuciyarsa cewa Allah tabaraka wa ta'ala shi kadai ne wanda aiyukan Halittu ke hanunsa da kuma umarnin tsarin rayuwar Halittu, kuma wajibi ga Bawa ya koma zuwa ga Ubangijinsa da Shugabansa shi kadai ba yada abokin Tarayya, kuma yin da'a da biyayya ga dukkanin al'amuransa musaman ma sakon da aka isar da shi garesu na wahayi da kuma hukunce-hukunce addinin, duk wanda ya yi Imani da wannan ya tsira daga bautar wanin Allah ko shirka a akidance. Wannan shi ne abinda Allah tabaraka wa ta'ala ya bayyana mana a yayin da yake umartar Annabinsa mai girma wajen isar da sako na Asalin kadaita Allah a bangaren bauta, a cikin suratu Ali Imrana Aya ta 64 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce (da su Ya Muhamadu) Ya Ku ma'abuta littafi, ku zo (da gaggawa) zuwa ga kalma mai daidaitawa tsakaninmu da ku, (ita ce) kar mu bauta wa (komai) sai Allah, kada kuma mu tara wani abu da shi, kuma kada shashinmu ya riki wani Shashi iyayengiji ba Allah ba,To idan suka ba da baya sai ku ce (musu) ku sheda da cewa mu Musulmi ne) a cikin suratu Yusuf Aya ta 39 da ta 40, Allah tabaraba wa ta'ala ya bayyana manufar kadaita Allah a bakin Annabinsa Yusuf amincin Allah ya tabbata a gareshi da Shugabanmu Annabi Muhamadou, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ya abokina na kurkuku, yanzu iyayen giji barkatai su suka fi, ko kuwa Allah Daya mai rinjaye?*Abin da kuke bauta wa wand aba shi ba, ba komai ba ne face wasu sunaye da kuka kago ku da iyayenku, wadanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba.Hukunci na Allah ne kawai, ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kadai.wannan shi ne addini mikekke, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka))

**************************Musuc**************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, tsira daga aikata shirka ko kuma hada Allah da wani a bangaren bauta ko bautawa wanin Allah a bangaren bauta a aikace shi ne yin Da'a ko biyayya ga wani wanda yi masa biyayya ba za ta kasance Da'a ga Allah madaukakin sarki ba kamar wasu abin bauta koma bayan Allah, ko kuma shugabanin bata wadanda mushrikai ke cewa wajibi ne a yi musu biyayya ba tare da wata hujja daga Allah madaukakin sarki ba, wannan shi ne abinda Aya ta 40 cikin suratu yusuf da ta gabata ta yi ishara da hakan,A cikin suratu Taubat Aya ta 30 da kuma ta 31 Allah madaukakin sarki ya ce:(Yahudawa sun ce Uzairu dan Allah ne, Annasara kuwa suka ce Al'masihu dan Allah ne wannan fadarsu ce kawai da bakunansu, suna kwaikyawon fadar kafirawan da suka gaba ce Allah ya tsine musu, ta kaka ake kautar da su daga gaskiya?Sun riki Malimansu da fada-fadansu da Almasihu Dan Maryamu iyayen giji maimakon Allah, alhali kuwa ba abin da aka umarce su sai su bauta wa Ubangiji Makadaicin sark, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi. Tsarki ya tabbata a gare shi game da abin da suke tara shi (da shi)).

A cikin Tafsirin Majma'ul Bayan, an ruwaito hadisi daga Ady bn Hatam Atta'I ya ce na je wajen ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayin da yuwana a kwai sarka dake dauke da gumkin yadda aka rataye Annabi Isa(a.s) kamar yadda kiristoci ke cewa wato sakandami sai Ma'aikin Allah (s.a.w) y ace da ni Ya Ady ka je ka cire wannan gumki daga wuyanka sai na je na cire sannan na dawo wajen Ma'aikin Allah yayin da yake karanta wannan Aya ta cikin suratu Tauba(Sun riki Malimansu da fada-fadansu da Almasihu Dan Maryamu iyayen giji maimakon Allah, alhali kuwa ba abin da aka umarce su sai su bauta wa Ubangiji Makadaicin sark, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi. Tsarki ya tabbata a gare shi game da abin da suke tara shi (da shi) suratu Tauba Aya ta 31 yayin da ya gama sai na ce mu fa ba ma bauta musu sai ya ce wadannan fada-fadan ba suna haramta abinda Allah halarta ba ne sannan kuma suna halarta abinda Allah ya haramata sannan kuma ana yi musu biyayya a hakan ? Sai na ce hakika haka ne, sai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare vda iyalan gidansa tsarkaka ya  ce wannan shi ne bautarsu) masu saurare, cikin littafin Usulul Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) a yayi da yake fassaka wannan Aya wato sun riki Sun riki Malimansu da fada-fadansu da Almasihu Dan Maryamu iyayen giji maimakon Allah, ya ce wallahi bai kira su zuwa bautar kansa ba, ko da ma ya kira su da ba su amsa masa ba wato bas u yi masa biyayya a kan hakan ba, sannan sun kasance masu halarta musu haram suna kuma haramta musu abinda yake halal ne a garesu, sannan su kuma suka yi biyayya a kan hakan, sai suka bauta musu ba tare da sun sani ba) har ila yau cikin Littafin na Kafi, an ruwaito Hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce :(duk wanda yayi wa wani Mutum biyayya a kan sabon Allah, hakika ya bauta masa), Aliyu bn Ibrahim cikin Tafsirinsa wanda aka fi sani da tafsiru Qummy ya ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) , hadisin ya nada tsaho sosai ,amma ga wani bangare nasa Imam (a.s) ya ce amma malimansu da fada-fadansu hakika sun rike su iyayen giji ta hanyar yi musu biyayya suka kuma bar Umarnin Allah tabaraka wa ta'ala da Littafinsa gami da Ma'aikansa sai suka jefa su bayansu, kuma hakika Maliman nasu da fada-fadansu ba su umarce su da su bi su ba, sai suka yi musu biyayya suka kuma sabawa Allah da ma'aikinsa, Hakika an Ambato wannan ne cikin Littafinmu domin ya kasance wa'azi a gare mu).

Masu saurare, cikin wannan Nassi da makamatansu, ya bayyana a gare mu cewa daga misdakin shirka ko bautar wanin Allah a aikace shine bin shugabanin Bata da Dawakit ko yaya suke a zahiri, na addinin ne ko kuma wasu na daban, matukar dai sun yi umarni da abinda Allah tabaraka wa ta'ala bai yi umarni da shi ba ko kuma abinda suke yi wa biyayya ya saba da abinda Littafin Allah gami da Sunar Manzon Allah (S.A.W)tare da na iyalan gidansa tsarkaka shi ma bautar wanin Allah ne ko kuma shirka ne.

Musuc

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.