kadaita Allah a Neman Taimako
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tanbayarmu ta yau ita ce minene aka nufin da kadaida Allah a neman taimako? Domin mun san cewa hakika Allah tabaraka wa ta'ala cikin suratu Fatiha ya wajabta mana kadaita shi a neman taimako kamar yadda ya wajabta mana kadaita shi a Ibada, inda ya ce (kai kadai muke bauta wa, kuma kai kadai muke neman taimakonka) suratu fatiha Aya 5, to ta yaya za mu kasance masu kadaita Allah a neman taimako kamar yadda muke kadaita shi a Ibada shi kadai bas hi da abokin tarayya,Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana a faifai.
************************Musuc****************************
Masu Saurare, kamar yadda shirin ya saba, duk tambayar da muka bijoro da ita mu kan komawa kan hankaken shiriya domin samun amsar mu, da farko ma'anar neman taimakon Allah madaukakin sarki a wajen masana da Arifai na hakikanin Littafin Allah mabayyani wato Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma iyalan gidansa tsarkaka, a cikin Tafsirur Majma'ul bayyan, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah Mustapha(s.a.w) ya ce:(Hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya hore mani suratu fatihatu Kitaf wato suratu fatiha, fadar Allah madaukakin sarki na cewa (kai kadai muke bauta wa,) ma'anar sa ihklali a bauta, amma fadarsa na cewa (kuma kai kadai muke neman taimakonka) shine mafi fifiko da falala ga abinda Bayi suka nema na biyan bukatunsu), Masu saurare cikin wannan hadisi mai albarka za mu fahimci cewa neman taimako ga Allah shi kadai it ace hanya mafi girma da Mumuni zai bi wajen tabbatar da aikinsa a aikace na cewa shi Allah madaukakin sarki shi kadaine mawadacin da kowa yake neman taimakonsa,shi ne mai jinkai , kuma shi ne mai iko a kan biyan bukatun bayinsa, shi kadai ne ake koma wa wajen sa domin neman biyan bukatu. Wannan ma'ana yana ishara ne kan wani hadisin kudisi da Shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya nakalto kamar yadda ya zo cikin Littafin Uyunul Akhbar, a cikinsa a kwai isharori na kyakkyawan sakamako da Albarkar dake tattare da Bautar Allah ta'ala haka zalika da kuma neman taimakonsa shi kadai tabaraka wa ta'ala. Imam Ridha (a.s) ya ce: daga Ma'aifana su kuma daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(idan Bawa Ya ce, Kai kadai ni ke bautawa, sai Allah madaukakin sarki ya ce Bawa na yayi gaskiya, ina shaida muku zan saka masa bisa bautarsa da Ladan da zai lullubesa ga dukkanin wadanda suka saba masa cikin bautarsa, sannan Imam Ridha (a.s) ya ce idan kuma Bawa Ya ce (kuma kai kadai muke neman taimakonka) Sai Allah tabaraka wa ta'ala ya ce a gare ni kadai ya nemi taimako, kuma gare ni kadai ya dogara, ina shaida muku zan taimake shi a kan Al'amuransa, kuma zan taimakesa a yayin tsananinsa wato yayin da ya shiga cikin tsanani kuma zan kama hanunsa ranar aukuwar wani abu wato lokacin da wani abu ya auku kuma yana tsananin neman taimako) domin haka a cikin wannan hadisi mai girma za mu fahimci cewa ma'anar neman taimakon ga Allah madaukakin sarki ta gumshi komawa Bawa gare shi a dukkanin Al'umuransa a lokacin tsanani da ma lokacin aukuwar wani abu na farin ciki ne ko kuma na jumami ne. har ila abin fahimta a cikin Ayar da ta gabata ma'anar tauhidi ko kuma kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren neman taimako ba ta kadaita kawai a bangaren Ibada ba ta gumshi dukkanin al'amuran Mutane.kuma wannan komawar ya danganta da yanayin Imanin Bawa na kadaita Ubangijinsa na cewa dukkanin al'amura na Allah ne kuma a hanunsa yake, shi ne mai iko na isarma Bawa ga dukkanin al'amuransa domin haka wannan I'itikadi ko kuma mu ce Imani da wadannan ababe da muka bayyana a baya shi ke ma'aunin Imani Bawa a aikace wato idan ya amince kuma yayi aiki a aikace. Idan kuma muka fahimce hakan masu saurare, zai bayyana gare mu cewa neman taimako a wajen Allakh madaukakin sarki kadai a ckaran kansa na daga cikin misdakin bautar Allah tabaraka wa ta'ala a bisa dukkanin ma'anarta. Na'am hakan kuma na tabbatuwa ne a yayin da Mumuni ya nemi taimakon Allah madaukakin sarki da niyar amsa umarnin Allah tabaraka wa ta'ala wajen yin neman taimakon sa shi kadai a ko wani al'amari daga cikin al'amuransa.
***************************Musuc********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da hadisin da shekh Tabrasi ya ruwaito cikin littafinsa Al-ihtijaj inda a cikin sa aka ce Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kasance yana fadawa sahabansa cewa (ku fadi fadar Allah (Ka kadai mu ke bautawa) ku ce mu na bautawa Allah daya, ba za muyi masa kishiya ba, kuma ba za mu roki wani Ubangiji koma bayansa) abin nura cikin wannan hadisi,shi ne yadda Ma'aikin Allah (s.a.w) ya sanya tauhidin ibada ko kuma kadaita Allah a bangaren Bauta daya daga cikin misdakin neman taimako ga Allah wannan kuma ita Addu'a. wato abinda Manzon Allah (s.a.w) yake bayyana mana cikin wannan hadisi shine daya daga cikin misdakin Ibada a bangaren Bauta, komawa zuwa ga Addu'a, Addu'a kuwa ita ce neman taimako daga Allah.
Hakika Ayoyin Alkur'ani mai tsarki da Hadisan Ma'aikin Allah (s.a.w) gami da na iyalan gidansa tsarkaka sun bayyana mana cewa Addu'a ita ce kwalluwar Ibada wato tushanta kuma daga cikin misdakinta wato Ibadar kamar yadda Ayoyi suke ishara da hakan, a cikin Suratu Gafiri Aya ta 60 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ubangijinku kuma ya ce,"Ku roke Ni zan amsa muku, Hakika wadanda suka yi girman kai, game da bauta min da sannu za su shiga Jahannama a Wulakance).Masu saurare wannan Aya na nuni da cewa kin yin Addu'a ya kuma juya baya wajen rokon Allah madaukakin sarki na daga cikin misdakin girman kai daga Bautar Allah tabaraka wa ta'ala, kuma karshensa shine wuta da azabar lahira. Kamr yadda karshen a Duniya zai kasance kaskanci da Hasara, har ila yau kamar yadda shahararen hadisin nan yake ishara da hakan( duk wanda ya neman taimako a wajen wanin Allah ya kaskanta, kuma duk wanda ya taimakawa Azzalumi kan zalincinsa Allah zai kumya ta shi a bisa wannan taimakon da ya yi na zalinci)
Masu saurare, takaicecciyar amsar tamabayarmu ta yau wato ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren neman taimakonsa shi kadai ita ce mu kasance masu kadaita Allah wajen neman alheri da taimako gami da neman biyan bukatu daga wajensa madaukakin sarki wajen yin Addu'a da saurensu domin a hanunsa yake dukkanin alheri da al'amura madaukakin sarki.da haka ne mukan bujoro da tambaya ta gaba wato minene misdakin neman taimako ga Allah madaukakin sarki a rayuwar mu ta yau da kulun. Kamar neman taimako da hakuri, tsayar da salla da kuwa waliyan Allah da sauransu daga cikin hanyoyin da Nassosi suka Ambato, wannan kuma shi ne abinda shirin na gaba zai tattauna a kansa.
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.