Aug 03, 2016 16:49 UTC

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan ma'anar neman taimakon Allah shi kadai a dukkanin al'umura,tambayar mu da yau kuwa it ace mine ne misdakin neman taimakon Allah shi kadai madaukakin sarki? Kafin amsar tambayar bari mu saurari wannan.

**************************Musuc*************************

Masu saurare, a shirin da ya gabata mun bayyana ma'anar neman taimako ga Allah shi kadai, inda muka bayyana cewa ma'anar kebance neman taimako ga Allah shi kadai madaukakin sarki da kuma kadaici shi a kan wannan, shi ne ya kasance makomarmu da kuma neman bukatar mu ta alheri gami da neman taimako a kan bautarsa da kuma dukkanin al'amuranmu tabarka wa'ta'ala.Hadisai da dama sun bayyana cewa neman taimakon Mumuni ga Allah madaukakin sarki shi kadai ita ce hanyar samun kari daga muwafaka ta Allah madaukakin sarki, ibadarsa gami da kiyaye Ni'imarsa wacce ya hore masa tare kuma da samun rabauta na nasararsa tabaraka wa ta'ala cikin jihadi guda biyu, babbar da karamin da kuma dukkanin al'amuransa,wannan ma'ana ita ce wacce shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya bayyana mana, a yayin da yake bayyana mana ma'anar Ayar da muke karanta a ko wata Rana da dama ta cikin suratu Fatihatou-l-kitabi, bayan ga hakan a cikin wannan Aya a kwai fahimta inhari taimako ga Allah tabaraka wa ta'ala kamar wajen bauta ga Allah tabaraka wa ta'ala.A cikin Littafin Man La Yahduruhul-fakih, Shekh Saduk  ya ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ridha (a.s) yayin da yake bayyani dangane da wannan Aya mai girma (kai kadai muke bauta wa, kuma kai kadai muke neman taimakonka) ya ce idan Bawa ya ce kai kadai muke bauta wa, ya na nufin godayinsa da kuma neman kusanci ga Ubangiji madaukakin wajen Ambaton sunansa da kuma ikhlasi gareshi a dukkanin aiyukansa, idan kuma ya ce kuma kai kadai muke neman taimakonsa yana nufin neman Karin taufikin da Allah ya yi masa da kuma bautarsa da kuma dawwama a kan ni'imar da Allah ya yi masa gami da taimakonsa)

Masu  Saurare, abin fahimta cikin wannan hadisi mai albarka shi ne daga cikin muhiman misdakin neman taimakon Allah madaukakin sarki da kuma rabauta da taimakonsa shine gudanar da ibadarsa kamar yadda ya umurta, da kuma yin riko da hukunce-hukuncensa wanda ya shar'anta a gare mu.hakan kuma shine abinda Shugabanmu Imam Hasan Askari (a.s) ya shiryar da mu cikin hadisin da aka ruwaito wanda yake bayani kan misdakin wannan Aya mai albarka (kai kadai muke bauta wa, kuma kai kadai muke neman taimakonka), hakika Allama Sayyid Sharafudin Alhusaini cikin littafin Sharhul Ayatul-Bahira ya ruwaito hadisi daga Imam Azzakiyul-Al-hasan-Al-Askari (a.s) y ace:(Allah tabaraka wa ta'ala y ace sun ce ya kai mai hallitta mai ni'ima  a gare su kai kadai muke bauta wa, (ma'na sun ce ) ya kai mai ni'ima a garemu  muna yi maka biyayya cikin ihklasi tare da kaskantar da kai babu riya ko kuma neman suna)a bangaren karshe na wannan Aya mai Albarka wato kaidai muke neman taimako a gare ka, imam (a.s) ya ce muna neman taimako bisa yi maka biyayya wayen gudanar da Bautarka kamar yadda ka umarce mu, muka kiyaye abinda ka hanemu da shi a wannan Duniyar ta mu, muna kuma neman tsari daga shaidani jefeffe, da dukkanin masu tawaye daga cikin Aljannu da Mutane batattu da azzalimai. Masu wanan hadisi na Shugaban Askari (a.s)yana ishara kan cewa kamalar neman taimakon Allah madaukakin sarki shi ne neman tsari daga gare shi daga wasiwasi na shaidan jefeffe da kuma shaidanun Mutane da Aljan domin su dukkaninsu suna kira na rashin meka wuya ga Al'amarinsa madaukakin sarki da kuma girman kai gare shi.

****************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan Aya ta 56 cikin suratu Gafiri, wacce take ishara da kan abinda Imam Hasan Askari (a.s) ya bayyana inda Allah madaukakin sarki yake cewa (Hakika wadanda suke yin jayayya cikin ayoyin Allah ba tare da wata Hujja ta zo musu b aba komai a cikin zukatansu sai girman kai ba kuwa za su same shi ba. Sai ka nemi tsari da Allah (ya kiyaye ka), hakika shi mai ji ne Mai gani ne) har ila yau za mu fahimci wannan ma'ana cikin ayoyin 200 da 201 cikin suratu A'arafi, a cikinsu a kwai shiryarwa na neman taimakon Allah wajen watsi da waswasin shaidani, ma'ana neman taimakon hasken Allah madaukakin sarki da zai fahimtar da mu hakikanin waswasin shaidan ta yadda za mu kauce masa Allah madaukakin sarki ya ce:(  Idan Kuma wani abu mai fizga na shaidan ya fizge ka sai ka nemi tsari daga Allah, hakika shi mai ji ne Massani*Hakika wadanda suka ji tsoron Allah lokacin da wani wasuwasi na shaidan ya darsar musu (a zuci) sai suka tuna (da Allah), sai ga su suna ganewa).

 Hakika cikin Littafin Khisal Shekh Saduk (R.A) ya ruwaito Hadisi daga Shugabanm Imam Ali, Shugaban Masu kadaita Allah (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya ce (idan wasiwasin shadani ya samu dayanku, ya nemi tsari daga Allah, sai y ace na amintu da Allah da ma'aikinsa mai ikhlasi wajen tseda  Addini).

Dangane da tafsirin Aya da ta gabata kuwa wani hadisi na daban ya yi ishara kan cewa ambaton Allah madaukakin sarki gami da neman tsari daga gareshi na fada cikin sabo suna tsare mutum daga fadawa cikin sabon Allah madaukakin sarki kuma ya amintu daga shi saboda taimakon Allah tabaraka wa ta'ala.

Masu saurare sakamakon da za mu dauka cikin Nassosi da suka gabata dangane da tauhidin Allah madaukakin sarki a bangaren Neman taimakon Allah yana tabbatuwa ne da al'amura guda biyu: Na farko riko da biyayar Allah tabarka wa ta'ala kamar yadda ya yi Umarni. Na biyu: neman tsari daga gareshi daga wasiwasin Shaidani, ta haka ne kuma Allah yake taimakawa Bayinsa wajen samun juriya a kan mikekkiyar hanya da kuma tsira daga wasiwasin Shaidan. Baya ga wannan a kwai Ayoyi da hadisai da dama suka shiryar da mu kan misdaki da kuma hanyoyin cimma Neman taimakon Allah shi kadai wanda kuma za mu karanto su a Maku mai zuwa da yardar Allah tabaraka wa ta'ala.

*******************************Musuc********************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.