Misdakin neman taimakon Allah shi kadai (2)
shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan ma'anar da kuma misdakin neman taimakon Allah shi kadai madaukakin sarki a dukkanin al'umura,kamar yadda muka bayyana a shirin da ya gabata Yau ma za mu zo muku da wasu Nassosi da suke bayyani dangane da wannan Maudi'I ? Kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari wannan.
**************************Musuc*************************
Masu Saurare kamar yadda muka bayyana a shririn da ya gabata, a yau za mu ci gaba ne dangane da misdakin kadaita Allah madaukakin sarki shi kadai wajen Neman taimako kamar yadda Allah Tabaraka wa ta'ala ya umarce mu a Aya ta 5 cikin Suratu Fatihatu Kitab, inda Allah tabaraka wa ta'ala ya ce (kai kadai muke bauta wa, kuma kai kadai muke neman taimakonka) A bayyane yake wannan Aya tana nufin katange Neman taimakon ga Allah madaukakin sarki shi kadai,kuma Hakika a shirin da ya gabata mun bayyana cewa misdakin kadaita Allah a bangaren neman taimako yana tabbatuwa ne da al'amura guda biyu su ne yin biyayya ga Allah da kuma bauta masa kamar yadda ya umurta, sai kuma neman taimakon sa tabaraka wa ta'ala daga wasiwasin shaidan ga dukkanin nau'o'insa.A shirin na yau za mu Ambato wasu misdakin na kadaita Ubangiji wajen neman taimako ga Allah shi kadai kamar yadda Nassosi suka Ambato.
Masu saurare kamar yadda Nassosi suka bayyana, Addu'a na daga muhiman hanyoyi neman taimako ga Allah madaukakin sarki shi kadai, hakika a shirin da ya gabata mun yi ishara dangane da hakan,kuma shakka babu Salla na daga cikin misdakin Du'a'I. A cikin Suratu Bakara Aya ta 45, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kuma ku nemi taimako (a kan gyraran kanaku)ta hanyar hakuri da kuma salla. Hakika kuwa ita (salla) ba shakka aba ce mai wuya, sai dai ga Masu tsoron (Allah))wasu daga cikin maluman tafsiri sun fassarar ma'anar salla a wannan Aya da Addu'a kamar yadda Allama jalil Muhamad bn Mas'oud Al'ayyashi cikin Tafsirinsa ya ruwaito wani hadisi daga Shugabanmu Iman Sadik (a.s) ya ce:(mi ne ne zai hana dayanku idan wani bacin rai ya same shi, ko kuma wata damuwa ta Duniya, ya yi Alwalla sannan ya shiga masallaci ya yi ra'aka biyu sai kuma ya roki Allah madaukakin sarki a kan ya yaye masa damuwarsa ko kuma bakin cikinsa, ba ku ji fadar Allah madaukakin sarki na cewa ba (Kuma ku nemi taimako (a kan gyraran kanaku)ta hanyar hakuri da kuma salla). A cikin Tafsirin Majma'ul Bayyan, Allama Tabrasi ya ce:Annabi Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan wani al'amari ya bata masa rai, sai ya nemi taimakon Allah ta hanyar salla da kuma Azumi).har ila yau cikin wannan Littafi na Tafsiri an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) Imam Ali (a.s) ya kasance idan wani al'amari na bacin rai ya same shi sai yin salla sannan kuma ya dinga karanto wannan Aya mai albarka(Kuma ku nemi taimako (a kan gyraran kanaku)ta hanyar hakuri da kuma salla).
Masu saurare, abin da ake nufi da Kalmar Sabr ko Hakuri cikin wannan Aya, Hakika hadissai da dama sun fassara ta da Azumi, a matsayin wannan ibada mai albarka wato ibadar Azumi ita ce ke karfafa iradar mutum,tana kuma daukaka ruhin gwagwarmaya da shaidangami da Nafsul lawwama, ta sanya mutum ya samu sabati ko dawwama a kan bautar Allah.A cikin Littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yayin da yake bayyana ma'anar wannan Aya (Kuma ku nemi taimako (a kan gyraran kanaku)ta hanyar hakuri ).sai ya ce abinda ake nufi da Hakuri shi ne Azumi).
**************************Musuc********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, shirin zai ci gaba a kan misdakin Hakuri cikin Ayar da ta gabata.Sayyid Sharafu-din Alhusaini cikin Littafinsa mai suna Sharhul-Ayatul-Bahira ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Hasan Askari (a.s) cikin wani Jami'in Hadisi yayin da yake tafsirin wannan Aya ya yi cikekken bayyani dangane da wani bangare na misdakin hanyoyin samun rabauta da taimako gami da nasarar Ubangiji.Imam (a.s) ya fadawa sauran kafirai, Yahudu da Mushrikai (Kuma ku nemi taimako (a kan gyraran kanaku)ta hanyar hakuri da kuma salla) ma'ana hakuri shi ne yin hakuri da aikata haram, da kuma tabbatar da Amanar da aka dauka, da Hakuri a kan jagorancin karya da kuma yarda da Annabi Muhamadu (s.a.w) a matsayin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma yarda da Aliyu bn Abi talib (a.s) a matsayin wasiyinsa , kuma nemi taimako ta hanyar hakuri a wajen yi musu hidima da kuma hidimar wanda suka umarce ku da yi musu hidima a kan neman cantcantar Yarda, Gafara gami da dawwama cikin Ni'imar Aljanna da kuma kusancin ga Arrahman da kuma kusanci tare da zababbun mumunai,gami da jin dadin na kallon shugaban Mursalai Muhamadou Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da kuma shugaban wasiyai Aliyu bn Abi Talib(a.s) gami da sauran shugabanin shiriya na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka, domon kalon su shi ke kara farin ganin 'yan Aljanna, yake kuma cika farincinsu , da kuma kamala shiriyarsu daga sauran ni'imomin Aljanna.
Masu saurare, kamar yadda muka ji wannan kyakkyawan bayyani daga Shugabanmu Imam Hasan Askari na albarkar da mai kadaita Allah madaukakin sarki zai cimma idan ya nemi dogoro da Allah madaukakin sarki shi kadai ta hanyar taimakon Hakuri a kan cikekken ma'anarsa kamar yadda Imam ya bayyana, wannan albarka na daga cikin fiyeyyen cikar alkwarin da Allah madaukakin sarki ya yi wa Mumuni.
Dangane da Ma'anar Neman taimako ta hanyar salla kuwa,misalin daya daga cikin misdakin neman taimakon Allah tabaraka wa ta'ala wanda aka yi umarni da shi cikin wannan Aya mai tsarki.Shugabanmu Imam Hasan Askari (a.s) ya bayyana mana misdakin sa da kuma cikekken ma'anarsa a yayin da yake bayyana cewa:(Ku nemi taimakon Allah ta hanyar yiwa Annabi Muhamadou (s.a.w) tare da iyalan gidansa tsarkaka Salati bisa kusanci na isa zuwa ga Aljannoni masu Ni'ima. Hakika yin salla na lokaci biyar da kuma yiwa Annabi Muhamadou gami da iyalan gidansa aminicin Allah ya tabbata a gare su salati, da kuma bin Umarninsu, imani da sirinsu da kuma abinda yake a bayyane nasu gami da kin saba musu (kamar cewa a'a ko kuma ya yaya) babban al'amari ne sai dai ga Masu tsoron Allah, masu tsoron ukubarsa wajen saba masa a kan abinda ya farranta ko kuma ya wajabta).
Masu saurare, abinda fahinta a shiri na yau, Addu'a, salla da kuma hakuri idan suka kasance bisa riko da wulaya daga Umarnin Allah madaukakin sarki ta hanyar yin biyayya da wulayar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma wulayar iyalan gidansa tsarkaka sune mafi girmar hanyar neman taimakon Allah shi kadai, da kuma kadaita shi madaukakin sarki.
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.