Sep 11, 2017 18:20 UTC

Kurdawa Da Yunkurin Ballewa Daga Iraki.                                                ( 2)

                              

A shirin baya mun bijiro muku da tarihin Kurdawan Iran na zamani wanda ya fara tun kafuwar kasar kamar yadda take a yanzu. Tarihi ne wanda yake cike da fadi tashi, musamman da suka sami kansu a cikin kasar da bata basu 'yanci na al'adu ta kowace fuska.

Gwamnatocin da aka kafa a kasar masu kishin larabci sun yi kokarin shafe al'adun kurdawan da maida su larabawa. A karkashin mulkin Sadam an hana kurdawa yin Magana da harshensu  a cikin wuraren na al'umma. Haka nan a makarantu ba a koyar da harshen nasu. Hatta tufafinsu na al'ada an yi zamanin da aka hana su daurawa a baina jama'a.

Dalilai irin wadannan da wasunsu sun tunzura kurdawa yin bore a kowace gomiya tun daga 1920 har zuwa 1980. Jagoran da ya yi fice a shigewa Kurdawan gaba a borensu shi ne Mustafa Barizani.

An yi yarjejeniya a tsakanin Kurdawan da gwamnatin Bagadaza a watan Maris na 1970 akan baiwa yankinsu 'yancin kwarya-kwarya. Amma iyakar waccan yarjejeniyar kan takardu bata fito fili a aikace ba.

Abinda ya biyo baya shi ne tilasta musu yin hijira daga garuruwansu na asali da kai su wasu yankuna masu nisa, tare da dauko larabawa da tsugunar da su a cikin garuruwan nasu. A karkashin siyasar larabci, an hana su radawa 'ya'yansu sunayen gargajiya sai dai na larabci.

 

Daga shekarar 1975 zuwa 1991 ne, Kurdawa suka rayu cikin tsanani mafi muni na tarihinsu. Baya ga matsin lambar da suka fuskanta, Sadam din ya tsara farmakin da ya kira " Anfal" wanda ya kallafawa dan kawunsu Ali Majid da aiwatar da shi. An kai wa garuruwan kurdawa hari da makamai masu guba. Saboda haka kurdawan suke kiran Ali Majid da "Ali Mai Guba."

Bayan da aka kifar da gwamnatin Sadam a 2003, kurdawan sun dan lumfasa saboda sun sami kwarya-kwaryar 'yanci a karkashin tsarin tarayyar Iraki. Yanakin nasu  ya sami ci gaba da fuskoki da dama. A karkashin sabon tsarin mulkin da aka rubuta na Iraki a 2005 an bayyana cewa; harshen kurdawa da kuma larabci suna tafiya ne kafada da kafada a matsayin harsunan kasar Iraki.

A hakikanin gaskiya a karkashin sabuwar Iraki, an baiwa Kurdawa matsayi na azo a gani. Kuma daga matsayin kurdawa wadanda ake yaki da su sun koma halartattun tsiraru. Sun sama masu iko da yankunasu na Dahuk da Sulaimaniyyah da Arbil.

A cikin yankin na kurdawa da akwai majalisar dokoki da pira minister da kuma ministoci.Haka nan kuma suna da 'yan sanda da kuma sojoji da sune Peshmarga.

Kuma kaso 17% na kasafin kudin Iraki ana bai wa Kurdawan ne. Kuma duk da wancan abubuwan da suka kebanta da su a yankinsu na kurdawa, suna kuma taka rawa a cikin gwamnatin tarayya. Suna da makamai a cikin kowace cibiya. Sune suke rike da mukamin shugaban kasar Iraki da kuma mataimaikin shugaban majalisar dokoki. Haka nan kuma suna da jakadu da dama na kasar Iraki, a kasashen waje. A cikin majalisar dokoki ta tarayya suna da kuejru 57 daya daga cikinsu ita ce ta mataimakin shugaban majalisar.

Faduwar Sadam ya kawo sauyi a cikin salon siyasar kasar ta  Iraki. "Yan Shi'a da suka rayu cikin killacewa sun shigo fagen siyasar kasar da karfi. Kudawa kuma daga wadanda ake kora da fada da su, sun koma masu jan wuya a siyasance. Su kuma ahlusunnan larabawa sun koma daidai da matsayin da ya dace da su a cikin kasar.

Ta fuskar rawar da kowane bangare yake takawa a siyasance, shi'a su ne a gaba da sama a fagen siyasar kasar. Sai Kurdawa da kuma ahlussuna a matsayin bangarori biyu.

Tare da cewa Kurdawan sun sami sauyi mai girma da daukakar da ta wuce wacce suke tsammani a karkashin Iraki, amma shugaban yankin na kurdawa, Mas'ud Barzani ya tsaida ranar 25 ga watan Satumba na wannan shekarar domin gudanar da kuri'ar raba gardama akan makomar yankin.

Tambaya mai muhimmanci anan ita ce wane amfani ballewa daga Iraki da kafa kasar Kurdawa yake da shi, mai makon ace Barzani da jam'iyyarsa sun ci moriyar yanayi na musamman da suke sami kansu a ciki a kasar ta Irakin.

                               

Batun ballewar yankin kurdawa tun bayan mamayar da Da'esh ta yi wa wasu yankunan kasar a 2014  ya fito fili dag abakunan jami'an yankin. Mas'ud Barzani yana daga cikin wadanda su ka fito fili suna Magana akan hakkinsu na ballewa da kafa 'yan tacciyar kasarsu ta Kurdawa. Kuma shi ne ya bijiro da batun yin kuri'ar raba gardama a yankin na Kurdawa domin zabarwa kansu makoma.

A cikin watan Febrairu na 2016 ya fadi cewa: "Kurdawa daidai su ke da sauran al'ummun gabas ta tsakiya za su iya samun hakkokinsu. Hakkoki ne da Allah ya basu kuma na dabi'a, babu wanda yake da ikon ya yi inkarin hakan."

A cikin watan Maris na wannan shekara ta 2017 Barzani ya kara fadin cewa: "Kasashen Yuguslavia da Cheslovakiya sun bace daga dorin kasa, a wannan lokacin ma abinda yake faruwa Kenan da yarjejeniyar Cisce Picko."

A karshe Barzani ya tsaida raanr 25 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2017 domin gudanar da kuri'ar raba gardama akan makomar yankin.

 

                                 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tags