'Yan Boko Haram Sun Kai Wasu Munanan Hare-Hare Kasar Kamaru
Majiyoyin tsaro a kasar Kamaru sun bayyana cewar cikin sa'oi 24 wasu mutane da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wasu hare-hare guda uku ciki kuwa har da dakile wani kokari na kai hari wani sansanin 'yan gudun hijira a arewacin kasar.
Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo wani babban jami'in sojin kasar ta Kamaru tsakanin shekarun jiya da jiya Talata maharan da ake zaton 'yan Boko Haram din ne sun kai hare-hare har sau uku a garin Darak da Diguina da kuma dakile wani harin da suka so kai wa sansanin 'yan gudun hijira na Kolofata a yankin Arewa mai nisa na kasar Kamarun.
A harin da suka kai garin na Darak, sun kashe mutane 6 ciki har da shugaban ofishin 'yan sandan yankin. Kamar yadda kuma maharan sun sanya wuta da kona gidaje a kauyen Diguina a lokacin da suka kai hari can.
Har ila yau majiyar tsaron ta bayyana cewar wata mace budurwa dauke da bama-bamai jikinta ne ta yi kokarin kai harin kunar bakin waje wani sansanin sojoji da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijirar, inda sojojin suka bindige ta lokacin da suka fahimci cewa 'ya ta'adda ce.
Wannan dai ba shi karon farko da 'yan Boko Haram din suke kai irin wadannan hare-hare a kasar ta Kamaru ba.