Libya: Tsarkake Cibiyar 'Yan ta'adda ta Karshe A Arewacin Libya
Sojojin Gwamnatin Libya Suna share yankin "Al-Jizah' daga yan ta'adda.
Kakakin rundunar sojojin da ake kira: "Bunyanun-Marsus" da ke karkashin gwmanatin hadin kan kasar Libya, Ridha Isa, ya ce; Sojojin suna share titunan yankin " al'Jizah" daga gyauron 'yan ta'adda.
Ridha Isa ta fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Yankin da su ke sharewa ne cibiya ta karshe da kungiyar Da'esh ta ke da ita a yankin arewacin kasar.
A ranar asabar da ta gabata ma dai kakakin sojan na "Bunyanun-Marsus" ya ce; sun kwace iko da dukkanin garin Sirta wanda ya dade a hannun 'yan ta'addar Da'esh.
Kungiyar ta Da'esh ta koma amfani da kai hare-haren kunar bakin wake da dasa bama-bamai a cikin sassan kasar ta Libya.