An Buda Iyakokin Kasashen Kamaru Najeriya Da Tchadi.
Bayan kwashe sama da shekara guda da rufe kan iyakar Kamaru da kasashen Tchadi da Najeriya saboda hare-haren kungiyar Boko haram, a wannan talata an bude kan iyakar.
Kafafen yada Labaran kasar Kamaru daga birnin Yawunde sun sanar da buke kan iyakar kasar da Najeriya gami da Tchadi a jiya Talata, wannan kuma na zuwa ne bayan nasarar da Dakarun hadin gwiwar kasashen suka samu inda suka fatattakin mayakan Boko haram daga yankin.
Rahoton ya ce a baya Mahukuntan kasar Kamaru sun sanar da bude wani bangare na iyakar kasar da kasashen Najeriya da Tchadi a karshen watan Nuwambar da ya gabata, to saidai bayan wannan sanarwa,mayakan kungiyar boko haram din sun kaiwa Dakarun kasar hari a sansanin su dake kan iyakar inda suka hallaka Sojoji guda shiga.
Mahukuntan na kamaru sun ce babu gudu babu ja da baya wajen sanya ido a kan wannan gagarumar nasara da Sojoji suka samu kuma za a ci gaba da kai farmaki kan maboyar 'yan kungiyar Boko Haram domin dawo da harakokin kasuwanci a kan iyakar kasar da Najeriya gami da Tchadi.
Hare-haren ta'addancin da mayakan kungiyar Boko haram ke kaiwa a yankin tabkin tchadi ya kasance babbar barazana ga tattalin arzikin yammacin Afirka musaman kasashen Kamaru Najeriya,da kuma Tchadi, lamarin da ya janyo koma baya sosai na shigar kudi ga aljihun Gwamnati ta hanyar Costom.