Tattauna Rikicin Siyasar Kasar Gambiya A Taron Kasar Mali
(last modified Sun, 15 Jan 2017 07:29:46 GMT )
Jan 15, 2017 07:29 UTC
  • Tattauna Rikicin Siyasar Kasar Gambiya A Taron Kasar Mali

Mahalarta taron kasashen Afirka da Faransa da aka bude a kasar Mali, ya tattauna halin da kasar Gambiya ta ke ciki.

Mahalarta taron kasashen Afirka da Faransa da aka bude a kasar Mali, sun tattauna halin da kasar Gambiya ta ke ciki.

Bayanin taron ya yi kira da a sami mika mulki cikin sulhu ba tare da wani rikici ba.

Daga cikin mahalarta taron da akwai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Ellen Johnson ta Liberia da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, sai kuma zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow.

Yahya Jammeh wanda ya yi shekaru 22 akan karagar mulkin kasar Gambiya, ya  sha kashi a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar farko ta watan Decemba na shekarar da ta gabata.

Bayan da ya yi furuci da samun nasarar abokin hamayyarsa Adama Barrow, ya janye inda ya bukaci a yi bincike akan sakamakon zaben.