Mutane 3 Sun Mutu Sakamakon Harin Ta'addanci A Kasar Kamaru
Jan 21, 2017 11:52 UTC
Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar alal akalla mutane uku sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin ta'addanci da aka yi arewacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya bayyana cewar a wani harin ta'addanci da aka kai yankin Kouseri da ke lardin arewacin Kamaru a daren jiya Juma'a mutane uku sun rasa rayukansu kana kuma wasu da dama sun sami raunuka.
Har ya zuwa yanzu dai ba a san wadanda suka kai harin ba, to sai dai kuma tun daga shekara ta 2009 ne kasar ta ke fuskantar hare-haren ta'addancin kungiyar Boko Haram don haka ne ma ake sanya yatsar zargi ga kungiyar.
Tags