Gwamnatin Libiya Ta Jaddada Bukatar Neman Dage Mata Takunkumin Sayan Makamai
Jan 29, 2017 12:25 UTC
Fira ministan gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ya jaddada bukatar neman dage wa kasarsa takunkumin sayan makamai.
A jawabinsa a zaman taron shugabannin kasashen Afrika da suke makobtaka da kasar Libiya a jiya Asabar: Fira ministan gwamnatin hadin kan kasa a Libiya Fayiz Assarraj ya jaddada yin kira ga kungiyar tarayyar Afrika da sauran kungiyoyin kasa da kasa kan su taimaka a hanzarta cire takunkumin da aka kakaba kan kasarsa na hanata sayan makamai.
Assaraj ya kara da cewa: Azamar da gwamnatin Libiya take da ita na ganin ta kawo karshen duk wani aikin ta'addanci a cikin kasarta lamari ne da ya dogara kan irin karfin makaman da take da shi.
Tags