An Cafke Mutane 700 A Libya Da Suke Shirin Tsallakawa Zuwa Turai
Jan 31, 2017 12:36 UTC
Jami'an tsaron kasar Libya da ke gadin iyakokin kasar sun sanar da kame mutane kimanin 700 da suke shirin tsallakawa zuwa nahiyar turai daga kasar ta Libya ba bisa ka'ida ba.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron sun rutsa da mutaten ne da suke shiga cikin wani kwalo-kwalo da zai tsallaka ruwa da daga gabar ruwan kasar Libya, wasu daga cikinsu sun tsere, yayin da aka kame wasu kimanin 700 daga cikinsu.
Bayanin kara da cewa dukkanin mutanne da aka kame bakin haure ne daga kasashen Afirka da ke kudancin ksahara, kuma babu wani da yake dauke da izinin shiga wata kasa daga cikin kasashen nahiyar turai.
Tags