Kamaru: An Kame Wasu Masu Garkuwa Da Mutane
(last modified Thu, 09 Feb 2017 12:24:56 GMT )
Feb 09, 2017 12:24 UTC
  • Kamaru: An Kame Wasu Masu Garkuwa Da Mutane

Majiyar Tsaron kasar Kamaru ta ce an kame wasu mutane biyar a yankin Ndokayo da ke gabacin kasar.

Majiyar watsa labaru ta Afirka Times, ta ambato majiyar tsaron kasar Kamarun na cewa; Jami'an tsaro na Genderma sun sami bindigogi da kuma wukake a tare da mutanen, haka nan kuma da riguna masu sulke.

Mutanen dai suna a matsayin wata kungiya ce wacce ta kware wajen satar mutane da yin garkuwa da su, domin karbar kudaden fansa.

Binciken farko ya nuna cewa idan sun sace mutane suna ketara iyaka da su zuwa kasar Afirka ta tsakiya, kafin su karbi kudaden fansa sannan su sake su.