Kasar Libiya Ta Bukaci Taimakon Soji Daga Kungiyar Tsaro Ta NATO
Gwamnatin kasar Libiya wacce Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita ta bukaci kungiyar tsaro ta NATO da ta taimaka mata da makamai da kuma horar da sojojin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a wata ganawa da yayi da manema labarai, babban sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya sanar da cewa ya sami takardar takardar wannan bukata ta kasar Libiya a jiya Laraba, sannan ana ci gaba da dubi don ganin wani irin taimakon za su iya ba wa gwamnatin Libiya.
Rahotanni sun ce daga cikin bukatar da gwamnatin Libiya ta gabatar wa kungiyar NATOn har samar da wasu cibiyoyi na tsaro da kariya a kasar Libiyan.
Tun dai bayan kawar da gwamnatin Kanar Mu'ammar Qaddafi a shekara ta 2011 bisa goyon bayan kungiyar NATOn kasar Libiya ta shiga halin rashin tsaro sakamakon tsoma bakin wasu kasashen waje cikin harkokin cikin gidan Libiya da kuma share fage wa kungiyoyin 'yan ta'adda shigowa kasar.