Shirin MDD na aiki tare da Ma'aikatar Shara'a ta kasar Gambiya
(last modified Thu, 02 Mar 2017 05:08:39 GMT )
Mar 02, 2017 05:08 UTC
  • Shirin MDD na aiki tare da Ma'aikatar Shara'a ta kasar Gambiya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shirin ta na aiki tare da Ma'aikatar Shari'a gami da kungiyoyin kare hakin bil-adama a kasar Gambiya

A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, Jafari Paltoman jami'in harakokin Siyasa a MDD ya ce idan magabatan Kasar Gambiya suka bukaci taimakon Majalisar wajen hukunta wadanda   suka aikata laifi a zamanin Gwamnatin Shugaba Jammeh, to Majalisar a shirye take tayi aiki tare da sabuwar Gwamnatin ta Gambiya.

Bayan ganawarsa da Shugaba Adama Barauw na Gambiya , Mista Jafari Paltoman ya ce sun tattauna ne kan batun tabbatar da sasantawa tsakanin 'yan siyasar kasar tare kuma da zartar da adalci a kan mutanan da suka aikata laifi a kasar.

Jami'in ya je birnin Banjoul ne tare da Muhamad bn Tchambas wakilin musaman na Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka da yankin Sahel.