Mar 11, 2017 19:07 UTC
  • Libya: Makaman Kasar Sun Fada Hannun 'Yan ta'adda.

Cibiyar bincike ta ( CAR) ta ce makaman da kasar Libya ta ke da su kanana da matsaita sun fada hannun 'yan ta'adda.

 Cibiyar bincike ta  ( CAR) ta ce makaman da kasar Libya ta ke da su kanana da matsakaita sun fada hannun 'yan ta'adda.

Cibiyar bincike da nazarin mai ofishi a kasar Birtaniya ta ce; kanana da kuma matsakaitan makamai na Libya an yi safararsu zuwa kasashn da su ke kudancin sahara inda su ka fada hannun kungiyoyin 'yan ta'adda.

Bugu da kari, rahoton ya ce 'yan kabilar Dawariq sun taka rawa wajen fasakwaurin makamai na Libya zuwa kasashen kudu da sahara da kuma kasashe kamar Libya da Iraki.

Kasashen Mali da Chadi da Ivory Coast, da jamhuriyar Afirka ta tsakiya suna daga cikin kasashen da makaman su ke isa.

Tags