A kwai yiyuwar hallakar 'yan Hijra da dama a tekun Libiya
Wata kungiyar agaji ta kasar Spaniya ta ce akwai fargabar cewa 'yan cin rani 200 sun mutu bayan da wasu kwale-kwale 2 suka nitse a gabar tekun Libya.
Kungiyar mai suna Proactiva Open Arms, ta ce ya zuwa yanzu an gano gawawwaki biyar suna yawo a kusa da kwale-kwalen biyu da suka kife, wanda kowannensu ke dauke da mutum sama da dari.
Kungiyar dai ta ce akalla 'yanci rani dari biyu da arba'in sun mutu, saboda yadda mutane suka yiwa kwale-kwalen yawa.
Ana samun karuwar 'yanci ranin da ke kokarin isa nahiyar turai daga Libya.
Hukumar da ke kula da 'yanci rani ta kasa da kasa ta ce fiye da 'yanci rani dubu ashirin sun isa Italiya a cikin shekarar da muke ciki, yayinda aka kiyasta cewa wasu dari biyar da hamsin da tara kuma ko sun mutu ko kuma sun bata a kan hanyarsu ta zuwa turan.