An Dakatar Da tace Man Fetur A Kudu Maso Yammacin Libiya
Man fatur din da ake tacewa a kudu maso Yammacin kasar Libiya an dakatar da shi sandiyar tushe wani bututun Mai da wasu 'yan adawa suka yi a kasar.
Wani Jami'i na Ma'aikatar Matatar Man fetir din Zawiya mai nisan kilomita 50 daga yammacin Tripoli ya ce a wannan Litinin 'yan adawa sun tushe bututun dake kai Dan Man fetin din zuwa Matatar daga rijiyoyin Mai na Alsharara, lamarin da ya sanya aka dakatar da tace Man fetir din a matatar ta Zawiya.
Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da 'yan adawar ke toshe bututun danyan man fetir din a wannan yankin domin a watan Maris din da ya gabata ma 'yan tawayen sun toshe wannan bututu, kafin daga bisani suka sassanta da Gwamnati kuma suka bari aka ci gaba da aikin.
A cewar Kamfanin Man fetir kasar ta Libiya NOC, kimanin ganga dubu 200 ne ake tacewa ko wata rana a wannan matata ta Azzawiya wato sama da kashi daya cikin hudu na yawan Man fetir din da ake tacewa ko wata rana a kasar.
Kafin faduwar Gwamnatin Kanal Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, kasar Libiya na tace ganga sama da miliyan daya da dubu 600 na danyan Man fetir ko wata rana, yanzu kuma kasar na tace ganga dubu dari bakwai ne kacal.