Zaman Taron Kasashe Masu Makwabtaka Da Libya A Aljeriya
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kan rikicin kasar Libya ya bayyana cewa,a yau za a fara gudanar da zaman taron kasashe masu makwabtaka da kasar Libya a kasar Aljeriya.
Kamfanin dillancin Sharq Al-ausat ya bayar da rahoton cewa, mazon musamman na majalisar dinkin duniya a kan rikicin Libya Martin Kobler ya fadi da jijjifin safiyar yau cewa, za a fara taron na yau ne a kasar Aljeriya, tare da halartar dukkanin kasashe masu makwabtaka da kasar Libya.
Ya ce babbar manufar taron dai ita ce tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Libya, da kuma komawar dukkanin bangarorin siyasa na kasar a kan teburin tattaunawa tare da warware matsalolinsu ta hanyoyi na siyasa da fahimtar juna, wanda dukkanin bangarorin siyasar kasar da suka hada da Khalifa Haftar duk sun amince da hakan.