Bincike Kan Laifufukan Da Aka Yi Kan Bakin Haure A Libiya
Kotun Hukunta manyan Laifuka ta kasa da kasa ta fara gudanar da bincike kan laifufukan da ake tabkawa kan 'yan gudun hijra a kasar Libiya
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Fatou Bensouda Babbar mai shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC, a jiya Litinin na cewa akwai duban 'yan gudun hijra na kasashen Afirka dake cikin mawuyacin hali a gidagen kurkuku na kasar Libiya daga cikin su akwai Mata da kananen yara.
Uwar gida Fatou Bensouda ta kara da cewa fyade, kisa , azabtarwa ya zamanto ba laifi ba ga jami'an tsaron gidajen Yarin na kasar Libiya.
Yayin da take bayyani kan yanayin tsaro a kasar ta Libiya,Babbar mai shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC, Fatou Bensouda ta ja hankali kan alakar dake tsakanin masu safarar Mutane da kuma yadda wadannan kungiyoyi ke bunkasa tare da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar ta Libiya.
Tun bayan faduwar Gwamnati Kanar Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, masu safarar mutane ke mumunar amfani da wannan dama wajen safarar Mutane daga yammacin kasar ta hanyar ruwa zuwa kasar Italiya.