An Kubutar Da Daruruwan Yan Gudun Hijra Daga Halaka A Tekun Libya
(last modified Mon, 19 Jun 2017 06:52:50 GMT )
Jun 19, 2017 06:52 UTC
  • An Kubutar Da Daruruwan Yan Gudun Hijra Daga Halaka A Tekun Libya

Jiragen ruwa na kasashen Italia da Espania sun kubutar da daruruwan rayukan bakin haure wadanda suka makale a cikin tekun Medeteranian kusa da kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ma'aikatar harkokin wajen kasar Espania tana fadar cewa jami'an tsaron cikin ruwa na kasar sun kubutar da rayukan yan gudun hijira 526 daga ciki har da mata 9 masu ciki da kuma yara kanana 9 daga halaka a cikin tekun Medeteranian.

A wani labarin kuma majiyar jami'an tsaron kan iyaka na ruwa na kasar Italia ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun ceci rayukan yan gudun hijira kimanu 800 a cikin  sawu 8 wadanda suka makale a cikin tekun Medeteranian a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa a cikin makon da ya gabata kadai jami'an tsaron kan iyaka na ruwa na kasar Italia sun tsamar da yan gudun hijira 1000 daga halaka. 

Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata yawan ya gudun hijirar da suke kwarara zuwa kasashen Turai ya karu so sai.