Gwamnatin Mali Ta Koma Kan Kujerar Tattaunawa Da 'Yan Tawayen Kasar
(last modified Sun, 25 Jun 2017 12:25:02 GMT )
Jun 25, 2017 12:25 UTC
  • Gwamnatin Mali Ta Koma Kan Kujerar Tattaunawa Da 'Yan Tawayen Kasar

Gwamnatin Mali ta sanar da cewa ta koma kan kujerar tattaunawa da bangaren 'yan tawayen kasar bayan dakatar da zaman tun a shekara ta 2015 da ta gabata.

Tun a shekara ta 2015 aka cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Mali da bangaren 'yan tawayen kasar amma aka dakatar da batun aiwatar da sharuddan sulhu har na tsawon shekaru biyu saboda da wasu dalilai, inda a jiya Asabar mahukuntan Mali suka gayyato bangaren 'yan ntawayen da nufin ci gaba da gudanar da tattaunawa a tsakaninsu.

Iylad Auf Muhammad daya daga cikin jagororin 'yan tawayen Mali ya yi furuci da cewa: Gayyatar da gwamnatin Mali ta yi musu domin farfado da batun sulhu ya zo a daidai lokacin da ya dace tare da fatan ganin zaman ya haifar da da mai ido.

Manazarta suna ganin halin tsaka mai wuya da kasar Mali ta shiga a fagen tsaro ne ya tilastawa mahukuntan kasar kokarin farfado da batun yarjejeniyar sulhun da aka cimma a baya tsakaninsu da 'yan tawayen.