Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Libiya A Shekara Mai Kamawa
(last modified Sun, 16 Jul 2017 18:50:41 GMT )
Jul 16, 2017 18:50 UTC
  • Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Libiya A Shekara Mai Kamawa

Shugaban Majalisar Shugabancin Kasar Libiya ya sanar da gudanar da zaben Shugaban kasa gami da 'yan Majalisa a shekarar 2018 mai kamawa.

Jaridar Alyaumu-Sabi'i ta kasar Masar ta nakalto Fa'iz Siraj Shugaban Majalisar Shugabancin gwamnatin hadin kan kasar Libiya a wannan lahadi yayin da yake gabatar da jawabi ya kira al'ummar kasar da su shiryawa gagarumin zabe a shekara mai zuwa domin sake gina kasar

Shugaban Majalisar Shugabancin Gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin da take yi na yaki da ta'addanci a kasar

Tun bayan da kungiyar tsaron Nato ta kifar da Gwamnatin marigayi kanar Mu'amar Kaddafi a shekarar 2011, kasar ta Libiya ta fada cikin rikci.