Gwamnatin Kasar Libya Zata Kara Yawan Danyen Man Fetur Da Take Haka
Majiyar gwamnatin kasar Libya ta bayyana cewa zuwa karshen wannan shekara ta 2017 zata kara yawan danyen man fetur da take haka zuwa ganga miliyon gusa da dubu 250.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Musatafa San'ullah shugaba kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, kamfanin yana da kudurin kara yawan man fetur da yake hada zuwa gangan 1,250,000 a karshen wannan shekara, sannan zuwa 1,500,000 zuwa karshe shekara ta 2018.
Mustafa San'ullah ya kammala da cewa a cikin shekaru 4 zuwa biyar masu zuwa kamfanin zai haka danyen man fetur ganga miliyon 2,100,000.
Kasar Libya dai tana daga cikin kasashen mafi yawan arzikin man fetur a yankin amma bayan faduwar gwamnatin Mu'ammar Kazzafi, mafiya yawan rijiyoyin man kasar sun dakatar da aiki ko kuma sun fada hannun yan ta'adda.
Kasar Libya tana cikin kungiyar kasashe masu arzikin man Fetur ta OPEC, sai dai dauke ta daga cikin yerjejeniyar rage yawan man Fetur da kasashen kungiyar suke haka don matsalolin tsaron da take fama da su.