Gabatar Da Shawarar Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Libiya
(last modified Thu, 20 Jul 2017 05:20:50 GMT )
Jul 20, 2017 05:20 UTC
  • Gabatar Da Shawarar Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Libiya

Shugaban Majalisar Shugabancin Kasar Libiya Fa'iz Siraj ya gabatar da shawarar magance rikcin kasar inda ya bukaci a gudanar da zaben Shugaban kasa da na 'yan Majalisa a watan Maris na shekarar 2018 mai kamawa.

Fa'iz Siraj ya tabbatar da cewa lokaci yayi da 'yan kasar za su hada kansu domin ceto kasar kuma a halin da ake ciki, kamata yayi ko wani gungu ya amince da sasantawa tare da dan uwansa domin kawo karshen yaki da rikicin cikin gidan, sannan kasar ta koma kan tafarkin konciyar hankali da zaman lafiya, domin haka ne ya gabatar da wasu shawarwayi da za su taimaka wajen cimma wannan manufa.

Daga cikin shawarwarin da ya gabatar Shugaban Majalisar Shugabancin kasar ta Lbiya Fa'iz Siraj ya bukaci da a gudanar da zaben Shugaban kasa gami da na 'yan Majalisa a watan Maris din shekarar 2018 mai zuwa, ganin cewa tsarin da kasar ke bi a yanzu ya sabawa bukatar Al'ummar kasar da kuma tafarkin Domokaradiya, domin haka Al'ummar kasar su zabi wanda suke ya dace da jagorance da kuma 'yan Majalisar da za su wakilci Al'umma akalla shekaru uku.

Fa'iz Siraj na gabatar da wannan shawarar ne a yayin da har yanzu kasar ke cikin rikici,a kwanakin da suka gabata, kungiyoyin 'yan ta'addar ISIS sun rasa sansanonin su a kasar bayan fafatawa da Dakarun tsaron kasar, kashin da 'yan ta'addar suka sha a yankin babbar koma baya ne ga kasashen yamma musaman ma Amurka da wasu kasashen Larabawa masu daukan nauyin ta'addanci a Duniya.

Cikin hirar da ta yi da jaridar Alkudusur Arabie Ra'id Salihat masaniya a harakokin siyasar kasar Libiya ta ce a kwai yiyuwar magabatan Watsinton na kokarin fadada mamayar da suke yiwa kasar Libiya domin cimma manunfin da suka sanya a gaba game da kasar, kuma a cikin makuni masu za a ga wannan batu a kasa, mai yiyuwa sake buda ofishin jakadancin Amurka a birnin Tripoli da kuma ganawar da jami'an Diplomasiyar kasar Amurkan suka yi da bangarori daban daban na cikin kasar gami da kara yawan Sojojin su a kasar na daga cikin wannan kudiri.

A bangare guda, kungiyoyin dake dauke da makamai dake samun goyon bayan wasu kasashen Larabawa da kasashen Yamma na ci gaba da yakin neman milki a kasar , duk da irin wannan yanayi magabatan kasar ta Libiya na ci gaba da tattaunawa da bangarori daban daban na kasar da kasashen waje domin taimakawa kasar ta samu zaman lafiya ,ziyarar da Babban Hafsan Sojojin kasar Khalifa Haftar ya kai  Hadaddiyar daular Larabawa tare da ganawarsu da magabatan kasar dangane da sayan makamai a bangare guda, sai kuma tattaunawar da magabatan kasar Rasha, ana iya bayyana shi a matsayin kokarin da magabatan Libiyar ke yi wajen dawo da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.

Jumullar wadannan sharuda da suka hada da ci gaba da neman milki daga bangarori daban daban na kasar, samun canji yanayi a yankin, a gefen haka kuma tarin arzikin karkashin kasa da kasar ke da shi, wacce ta kasance ke da rabin arzikin Nahiyar Afirka, da kuma wurin da kasar take a gefen tekum Bahrum, akwai hatsarin rarraba kasar kashi kashi, wanda hakan ya sanya kasar ta zamanto wurin wasan kura na kasashen yamma.

To amma duk da hakan, shawarar da Shugaban Majalisar Shugaban kasar ya bayar, ita hanya daya cilo da za ta kalubalanci duk wani hadari da rarrabuwar kasar, da kuma dawo da zaman lafiya gami da konciyar hankali, to saidai zartar da wannan shawara tana bukatar hadin kai na kungiyoyin siyasa, kalibu da ma Al'ummar kasar baki daya.