Gwamnatin Mali Ta Tabbatar Da Kama Wani Kasurgumin Dan Ta'adda A Timbuktu
Ministan tsaron kasar Mali Janar Salif Traoré ya bayyana cewar dakarun kasar tare da taimakon na kasar Faransa sun sami nasarar kama wani babban kusa a kungiyar masu dauke da makamin nan ta Macina Liberation Front da ta jima tana kai hare-hare kan 'yan kasashen waje da kuma wasu cibiyoyin kasar Malin.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo Janar Salif Traoré yana fadin cewa ina tabbatar da cewa jami'an tsaro sun sami nasarar kama dan ta'adda Alhousseyni Ag Assaleh wanda shi ne jami'an tsare-tsare na wannan kungiya wacce Amadou Koufa ke wa jagoranci a wani samame da suka kai yankin Timbuktu a ranar 8 ga watan Yuli.
Ministan ya kara da cewa an boye labarin kama dan ta'addan ne saboda kokarin da ake ci gaba da yi na kama sauran 'yan kungiyar.
Ita dai wannan kungiya ta Macina Liberation Front, wacce take da helkwatarta a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Malin, tana karkashin jagorancin wani malami ne mai suna Amadou Koufa wanda kuma ya kirayi magoya bayansa da su dau makamai don sake kafa daular Fulani ta Massina a kasar.