Sojojin Kasar Aljeriya Sun Halaka Yan Ta'adda Masu Yawa
(last modified Mon, 31 Jul 2017 14:56:46 GMT )
Jul 31, 2017 14:56 UTC
  • Sojojin Kasar Aljeriya Sun Halaka Yan Ta'adda Masu Yawa

Ma'aikatar tsaron kasar Algeria ta bayyana cewa sojojin kasar sun halaka yan ta'adda 6 a wata unguwa a kudancin birnin Algies babban birnin kasar a yau litinin.

Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya ce sojojin sun kashe yan ta'addan ne a unguwar Safasafah a garin Tiboze daga kudancin Algies.

Ma'aikatar ta ce ta fara shirin kakkabe yankunan kudancin Algies daga yan ta'adda ne tun ranar 23 ga watan Yuli da muke ciki, kuma ya zuwa yanzu sun halaka yan ta'adda 8 . Labarin ya kara da cewa  an kashe yan ta'adda 71 an kuma kama wasu 23 tun farkon wannan shekara. 

Tun bayan faduwar gwamnatin Mu'ammar Qazzafi a kasar Libya a shekara ta 2011 ne, ayyukan ta'addanci suka zama matsala ga kasashen da suke makobtaka da ita, musamman kasashen Algeria da Tunsia. Sannan faduwar biranen Haliba da Musil a kasashen Siriya da Iraqi sun sa yan ta'adda daga kasashen larabawa da dama suka fara komawa gida , inda suke zama matsala ga kasashen nasu.