Kasashen Jamus Da Faransa Zasu Karfafawa Na G5 Gwiwa
(last modified Tue, 01 Aug 2017 18:19:11 GMT )
Aug 01, 2017 18:19 UTC
  • Kasashen Jamus Da Faransa Zasu Karfafawa Na G5 Gwiwa

Kasashen Jamus da kuma Faransa sun sha alwashin karfafawa kasashen yankin Sahel wajen yaki da mayakan dake ikirari da sunnan jihadi.

Wannan bayanin ya fito ne ta bakin ministar harkokin tsaron ksar Jamus, Ursula Von Der Leyen, a yayin ziyara data kai yau Talata  Bamako babban birnin kasar Mali.

Ministar ta ce sun tattauna da hukumomin kasashen biyar da suka hada da Chadi, Nijar, Mali, Burkina faso da kuma Mauritaniya musamen kan batun karfafawa rundinar hadin gwiwar da kuam basu horo .

Misis  Der Leyen ta bayyan ahakan ne a yayin ganawarta  da shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Keita a Bamako a matakin karshe na ran gadin da suka soma da iata da takwararta ta Faransa a kasashen sahel.

Wannan ziyara dai na zuwa ne kwanaki shida bayan mutuwar wasu sojojin Jamus biyu sanadin hadarin wani jirgin sama mai saukar ungulu a arewacin kasar ta Mali.