MDD Ta Sanar Da Sunayen Kasashen Da Suke Fataucin Makamai Zuwa Libya
A cikin wani sabon rahoto da ta fitar, MDD ta bayyana kasashen Amurka, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar Da Turkiyya a matsayin kasashen da suke tura makamai kasar Libiya.
A cikin wani rahoto da ta fitar, tashar talabijin din Al-Mayadeen da ke watsa shirye-shiryenta daga Labanon, ta ce a cikin wani sabon rahoton da MDD ta fitar ta bayyana cewar duk da kudurin da ya haramta aikawa da makamai kasar Libiya, amma ana samun wasu mutane da wasu kasashe da suke aikawa da makamai Libiyan don amfanin kungiyoyi masu dauke da makami a kasar.
Rahoton ya ce cikin rahoton na MDD wanda ya kumshi binciken da aka gudanar tsawon shekarun 2014 da 2015 an gano cewa kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar da Turkiyya suna aikawa da makamai zuwa Libiyan, kamar yadda kuma akwai wasu kamfanonin kera makamai na Amurka da su ma suke aikewa da makaman zuwa Libiyan.
Tun dai bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011 kasar Libiyan ta shiga cikin mawuyacin hali na tsaro da rashin takamammiyar gwamnati sakamakon taimakon makamai da wasu kungiyoyi masu dauke da makami suke samu.