Sojojin Libya Sun Kame' Yan Kungiyar Ta'addanci Ta Da'esh Su 7
Aug 10, 2017 12:25 UTC
Jami'in sojojin Libya janar Mahmud Sharif al-Hashimy ne ya sanar da kame 'yan kungiyar ta Da'esh, a jiya laraba a garin Sabha da ke kudancin kasar.
al-Hashimy wanda shi ne kwamandan runduna ta 160 ta sojan kasa na Libya, ya ci gaba da cewa; Wadanda su ka kame din sun fito ne daga kasashe daban-daban da suka hada Masar, Tunisiya, da Aljeriya.
A daidai lokacin da kungiyar ta Da'esh take shan kashi a cikin kasashen Iraki da Syria, suna kokarin maida Libya zama wata muhimmiyar cibiyarsu.
Libya ta fada cikin rikici tun bayan faduwar gwamnatin Mu'ammar Khaddafi a 2011.
Tags