Senegal Zata Mayar Da Jakadanta Zuwa Birnin Doha Na Qatar
Gwamnatin kasar Senegal zata maida jakadanta zuwa birnin Doha na kasar Qatar bayan ta kirashi zuwa gida don shwaratawa a dai dai lokacinda kasar ta fara samun matsala da mokontanta.
Tashar television ta Al-Jazeera ta kasar Qatar ta nakalto Ahmad bin Saeed Al-ramihi kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa hakan ya biyo bayan tattaunawar shugaban kasar Senegal Maky Sall tare da sarki Tamim bin Hamd bin Khalifa ali-shani ta wayar tarho.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasra Qatar ya ce nan ba da dadewaba jakadan kasar Senegal zai dawo birnin Dohah kuma kasashen biyu zasu kara bunkasa dangartaka tsakaninsu a bangarori da dama.
Kasashen Saudia, Bahrain, Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Masar sun yanke huldan jakadancinsu da kasar Qatar sun kuma dora mata takunkumai na ziraga zirgan jiragen sama da na kan iyakoki tare da zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci.
Gwamnatin kasar Qatar da musanta dukkan zarge zargen da ake mata, kuma ta kara da cewa wadan nan kasashen suna son kwace diyaucinta ne sabota taki tafiya da su a kan wasu manufofinsi a yankin.