Gwamnatin Kasar Turkiyya Ta Mika Yan Ta'adda Ukku Ga Kasar Tunisia
(last modified Sat, 26 Aug 2017 12:47:37 GMT )
Aug 26, 2017 12:47 UTC
  • Gwamnatin Kasar Turkiyya Ta Mika Yan Ta'adda Ukku Ga Kasar Tunisia

Kakakin kotunan na musamman don hukunta yan ta'adda a kasar Tuniya ya bada sanarwan cewa kotunan sun karbi yan ta'adda guda ukku daga kasar Turkiya kuma sun jefa su a cikin kurkuku a kasar.

Tashar television ta وسیا‌الیوم ta kasar Rasha ta nakalto Sufyan Assulaity yana fadar haka, ya kuma kara da cewa wadannan mutanen ukku wadanda bai bayyana sunayensu ba, sun sami horon soje a cibiyoyin horar da sojoji na kungiyar Daesh a kasashen Iraqi da syria sannan sun shigi cikin fafatawan da akayi da sojojin kasashen biyu. 

Assulaidy ya kara da cewa mutanen suna da masaniya kan yadda ake shigo da yan ta'adda cikin wuraren da ake rikici.

A cikin watan da ya gabata ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunisia ta bayyana cewa tana da masani kan cewa yan kasar kimani dubu 2,929 suna yaki da gwamnatocin kasashen Syria da Iraqi, sannan wasu 800 kuma sun dawo gida, inda a halin yanzu jami'an tsaro suna sanya ido a kan kai kawonsu.