Aljeriya: An Kame 'Yan Adawar Siyasa Masu Yawa
(last modified Thu, 07 Sep 2017 18:07:34 GMT )
Sep 07, 2017 18:07 UTC
  • Aljeriya: An Kame 'Yan Adawar Siyasa Masu Yawa

Jami'an tsaron kasar ta Aljeriya sun kame 'yan hamayyar ne da suke yin kira ga shugaba Abdulaziz Buteflika da ya yi murabus.

Shugaban jam'iyyar ' Al-Jailul-Jadid' ta 'yan hamayya, Sufyan Jaylani ya yi suka akan kame membobin jam'iyyar tasu da suka hada da Nuruddin Ukriyav, wanda dan kwamitin koli ne na jam'iyyar kuma magatakardanta.

Sai dai Sufyan Jaylani ya ce an saki Ukriyav bayan sa'oi biyar da kama shi.

Jam'iyyun Jailul-Jadid, da Tala'ilul-Hurriyat sun kira yi pira ministan kasar Ali Bin Pelis da ya yi aiki da ayar doka ta 102 ta kundin tsarin mulkin kasar, domin sauke shugaba Buteflika daga kan shugabancin kasar bisa dalilin rashin lafiya da kasa tafiyar da harkokin kasa.

Wannan matakin na 'yan hamayya ya jawo musu suka daga 'yan majalisar dokokin kasar.