Kasar Chadi Ta Janye Dakarunta Da Ke Yakar Boko Haram A Nijar
Gwamnatin kasar Chadi ta fara janye daruruwan sojojinta da suke yaki da Boko Haram a yankin Diffa na kasar Nijar lamarin da ake ganin zai iya raunana fadar da ake yi da 'yan ta'addan na Boko Haram a Nijar da ma yankin baki daya.
Kafafen watsa labarai sun jiyo majiyoyin kungiyoyin ba da agaji a yankin na Diffa suna fadin cewa sojojin Chadin sun fara janyewa daga yankin lamarin da ya sanya mutanen wajen damuwar yiyuwar sake dawo da ayyukan 'yan kungiyar ta Boko Haram wadanda aka raunana su sosai.
Duk da cewa har ya zuwa yanzu dai gwamnatin Chadin ba ta ce komai ba, to amma dai wasu suna ganin hakan yana da alaka da haramcin tafiya Amurka da gwamnatin Trump ta kakaba wa 'yan kasar Chadin wanda tun a lokacin gwmanatin ta ce dokar tana iya shafar hadin gwiwan da kasar take bayarwa a wajen fada da kungiyar Boko Haram ciki kuwa har da kasantuwar sojojinta cikin ayyukan fada da Boko Haram din da Amurkan take goyon bayan a yankin.
Bayan mummunan harin ta'addancin da aka kai garin Bosso da ke yankin Diffa din a shekara ta 2016 ne kasar Chadi ta tura sojojinta guda 2000 zuwa kasar Nijar don taimakawa wajen fada da kungiyar Boko Haram din; duk da cewa daga baya dai adadinsu ya ragu sakamakon matsalolin da suke fuskanta musamman matsalar tattalin arziki da kasar Chadin take fuskanta.