Mayakan Kungiyar Yan Ta'adda Ta Daesh Sun Kai Hari A Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25169-mayakan_kungiyar_yan_ta'adda_ta_daesh_sun_kai_hari_a_kasar_libya
Wasu majiyoyin sojojin kasar Libya sun bada labarin cewa mayakan kungiyan yan ta'adda ta Daesh sun kai farmaki kan wani barikin sojoji a garin Ajdabia daga gabacin kasar a yau Laraba.
(last modified 2018-08-22T11:30:54+00:00 )
Oct 25, 2017 18:56 UTC
  • Mayakan Kungiyar Yan Ta'adda Ta Daesh Sun Kai Hari A Kasar Libya

Wasu majiyoyin sojojin kasar Libya sun bada labarin cewa mayakan kungiyan yan ta'adda ta Daesh sun kai farmaki kan wani barikin sojoji a garin Ajdabia daga gabacin kasar a yau Laraba.

Tashar television ta Sky News ta nakalto majiyar barikin sojoji na rundunar ta 152 a Ajdabiya tana cewa mayakan na kungiyar Daesh sun kawo hare-haren a safiyar yau Laraba kan sojoji wadanda suke bincike a kan wani titu kusa da barikinsu a garin Ajdabi sun kuma kashe sojoji 10.

Banda haka mayakan na Daesh sun kona dukkan motoci da kuma rumfar binciken na sojojin  sannan suka arce.