Nov 08, 2017 06:13 UTC
  • Bakin Haure Fiye Da 70 Ne Suka Halaka A Gabar Tekun Libiya

Bakin haure fiye da 70 ne suka halaka a cikin tekun Mediterranean kusa da gabar tekun Libiya a kokarinsu na neman tsallakawa zuwa kasashen yammacin Turai.

Rahotonni sun bayyana cewa: Wani kwale-kwale  dauke da bakin haure kimanin 120 a tekun Mediterranean da ke kan hanyarsa ta tsallaka tekun zuwa  kasar Italiya ya kife a kusa da gabar tekun Libiya da ke yankin Sai'da kusa da birnin Tripoli fadar mulkin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar halakar mutane 73.

Rahotonnin sun kara da cewa: Dakarun kula da gabar tekun na Libiya sun yi nasarar tseratar da bakin haure 47 da suka hada da mata 16 da wani karamin yaro guda.

Tags