An gano ramuka dauke da gawarwaki 400 a Iraki
(last modified Sun, 12 Nov 2017 05:51:33 GMT )
Nov 12, 2017 05:51 UTC
  • An gano ramuka dauke da gawarwaki 400 a Iraki

Gwamnan jihar Karkuk na kasar Iraki ya ce an gano wasu manyan kaburbura wadanda suke dauke da gawarwakin mutane 400 a wani wuri da ke kusa da garin Hawija, inda a nan ne aka fatattaki mayakan kungiyar IS a makon da ya gabata.

Hukumar gidan radio da telbijin na kasar Iran ya na nakalto gwamnan yankin Karkuk Rakan Saed a wannan Asabar na cewa an gano ramukan ne a sansanin sojin sama da ke arewacin Iraki.

Gwamnan  ya ce an gano ramukan ne bisa taimakon mazauna garin kuma wasu daga cikin mutanen da aka kashe na sanye ne da tufafin wandanda mayakan IS suka yanke ma hukunci kisa, yayin da sauran na sanye ne da tufafi fararen hula.

Wani mazaunin garin ya ce a cikin shekaru uku da garin ya kasance karkashin ikon kungiyar IS, 'yan ta'addar sun zartar da kisa ga 'yan gidan kurkuku wasun su kuma sun kona su da wuta.

Hawija ce  na daga cikin tunkar mayakan 'yan ta'addar IS da dakarun iraki suka tsarkake a farkon watan oktoban shekarar da muke ciki.