Kamaru: Bama-bamai Sun Fashe A Yankin Masu Magana Da Ingilishi
Majiyar gwamnatin kasar ta Kamaru ta ce a jiya lahadi da dare ne bama-baman guda hudu suka fashe a garin Bamenda.
Kamfanin dillancin labarun Faransa da ya dauko labarin ya ce harin bai haddasa wata asara ba ta rayuka ba.
Yankin da ke magana da harshen Ingilishi a kasar Kamaru na yin koke dangane da kokarin gwamnatin kasar na raba su da al'adunsu da kuma damfara musu harshen faransanci. Bugu da kari yankin yana koken cewa an mayar da shi saniyar ware wajen tafiyar da harkokin kasar.
Mutanen yankin sun kai kaso 20% na jumillar al'ummar kasar da ta kai miliyan 20.
A farkon watan Oktoba na wannan shekarar an yi taho mu gama a tsakanin jami'ar tsaron kasar ta Kamaru da kuma mazauna yankin da suka yin kira ballewa domin kafa kasarsu mai cin gashin kanta.