Kungiyar Ma'aikatan Tunusiya Ta Soki Kungiyar Kasashen Larabawa
(last modified Wed, 22 Nov 2017 11:24:10 GMT )
Nov 22, 2017 11:24 UTC
  • Kungiyar Ma'aikatan Tunusiya Ta Soki Kungiyar Kasashen Larabawa

Babban saktaren kungiyar ma'aikatan tunusiya ta soki kungiyar kasashen larabawa a game da matakin da ta dauka a kan kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon.

A cikin wani jawabi da ya gabatar jiya Talata Noruddin Taboubi, babban sakataren kungiyar ma'aikatan kasar Tunusiya ya ce matsayar da kungiyar kasashen larabawa ta dauka a taron ministocin harakokin wajen kasashen larabawa na kiran kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon 'yar ta'adda yiwa haramtacciyar kasar Isra'ila aiki ne.

Taboubi ya kara da cewa duk da irin sabanin mazhaba da siyasa da suke da shi tare da kungiyar hizbullah, matsayarsu a game da gwagwarmaya ba zai canza ba.

Har ila yau saktaren na kungiyar ma'aikatan Tunusiya ya ce za su ci gaba da goyon bayan duk wasu kungiyoyin gwagwarmaya masu fada da haramtacciyar kasar Isra'ila.

A ranar lahadin da ta gabata ce, ministocin harakokin wajen kasashen larabawa suka gudanar da taro a birnin Alkahira ba tare da halartar ministocin kasashen Qatar, Oman, Algeria, Labnon da Iraki ba.