'Yan Majalisar Tunusiya Sun Soki Sanarwar Bayan Taron Kungiyar Larabawa Kan Hizbullah
Wani adadi mai yawa na 'yan majalisar dokokin kasar Tunusiya sun yi Allah wadai da sanarwar bayan taron kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa kan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon suna masu kiran gwamnatin kasar da ta janye amincewar da ta yi da sanarwar.
Tashar talabijin din Al-Mayadeen ta kasar Labanon cikin wani rahoto da ta watsa ta bayyana cewar wasu 'yan majalisa 41 daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Tunusiyan, cikin wata takarda da suka sanya wa hannu, sun bayyanar da rashin amincewarsu da sanar bayan taron baya-bayan nan da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawan suka fitar inda suka bayyana kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a matsayin kungiyar ta'addanci, inda suka bukaci ma'aikatar harkokin wajen kasar da ta janye amincewa da wannan sanarwar da ta yi.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kungiyar Ma'aikata ta kasar Tunusiyan Nuruddeen Al-Tubibi ya bayyana cewar wannan matsaya da kungiyar Larabawan ta dauka wani lamari ne da babu wanda zai amfana da hakan in ba haramtacciyar kasar Isra'ila ba.
A ranar 19 ga watan Nuwamban nan ne dai kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa ta gudanar da wani zama a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, bisa bukatar kasar Saudiyya inda suka bayyana kungiyar Hizbullah din a matsayin kungiyar ta'addanci. Kasashen Qatar, Labanon, Oman, Aljeriya da Iraki sun kaurace wa zaman.