'Yan Hijira 250 Sun Tsira Daga Mutuwa A Gabar Ruwan Kasar Libya
Dec 16, 2017 19:10 UTC
Jami'an gwamnatin Libya sun sanar da tseratar da yan gudun hijira 250 da suke cikin kananan kwale-kwale.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato cewa; A cikin 'yan gudun hijirar sun kunshi mata da kanan yara da su ka fito daga kasashen Afirka da kuma kasashen larabawa.
Kasar Libya daya ce daga cikin hanyoyin da 'yan gudun hijira masu son shiga turai su ke ratsawa ta cikinta. Sai dai sau da yawa suna fadawa cikin matsalolin halaka akan doron ruwa, ko kuma sayar da su a kasuwar bayi a cikin kasar ta Libya.
A watan da ya gabata ne dai kafafen watsa labaru suka bankado kasuwar bayi da aka bude a kasar ta Libya, da ake sayar da bakaken fata.
Tags