Harin Boko Haram Ya Hallaka Mutane Uku A Kamaru
Majiyoyin kasar Kamaru sun sanar da mutuwar mutane uku a wasu tagwayen hare-haren ta'addanci da kungiyar Boko Haram ta kai a arewacin kasar Kamaru.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto wasu majiyoyin yankin arewacin kasar Kamaru na cewa harin farko an kai shi a yankin Mayo Moskota kusa da kan iyakar kasar da Najeriya yayin da mayakan Boko Haram suka shiga garin Zaneme inda suka kashe mutane biyu.
Hari na biyu kuma an kai shi ne a garin Kerawa-Mafa dake cikin yankin tare da kashe mazaunin garin guda.
A cikin 'yan kwanakin nan na karshen shekarar 2017, yankunan arewacin kasar ta Kamaru dake kan iyaka da Najeriya na fuskantar hare-haren kungiyar Boko Haram, inda ko a farkon makon da ya gabata sai da mayakan na Boko Haram suka kai wasu tagwayen hare-hare a yankin tare da kashe mutane uku.