Libya: An Fara Rijistar Masu Zabe
Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Libya ya ce duk da matsalar da ake fuskanta a kasar, amma an fara gudanar da rijistar masu zabe.
Jaridar al-Hayat a shafinta na Internet ta ambato dan sakon na MDD Gassan Salamah yana cewa; a shirye suke su taimaka wajen ganin an sami karin masu yin rijistar domin ya dara na zaben da ya gabata a kasar ta Libya wanda bai wuce kaso 17%.
Salamah ya kara da cewa; Duk da cewa rijistar tana tafiya sannu a hankali, sai dai duk da haka an sami karuwar masu rijistar da kaso 4% idan aka kwatanta da ta baya.
A shekarar 2018 ne ake sa ran gudanar da manyan zabuka a kasar ta Libya. A halin da ake ciki a yanzu kasar tana tafiya ne a karkashin gwamnatin hadin kan kasa.