An Ceto Daruruwan Bakin Haure A Kusa Da Gabar Ruwan Libiya
Jami'an Tsaron Ruwan Libiya sun sanar da ceto daruruwan bakin haure a kusa da gabar ruwan kasar.
Tashar Talabijin din Aljazera ta nakalto jami'an tsaron Libiya na cewa sama da bakin haure 350 ne dake kokarin zuwa kasashen Turai ta hanyar tekun Bahrum suka ceto daga hallaka a kusa a gabar ruwan kasar.
A yayin da suke ishara kan nutsewar kwale-kwale uku dake dauke da bakin hauren, jami'an tsaron ruwan Libiyan sun tabbatar da cewa mutanan da aka ceto an isa da su zuwa birnin Tripoli, inda yanzu haka ake tsare da su a wani wuri na musaman.
Kasar Libiya dai ta kasance wata hanya da bakin haure ke amfani da ita wajen shiga kasashen Turai, masu safarar mutane suna amfani da matsalar rashin tsaro da kasar ta Libiya ke ciki wajen ficewa da su zuwa kasashen Turai.