An Gargadi Kasar Italia Kan Ta Guji Kawo Sojojinta Cikin Kasar Libya
(last modified Sat, 20 Jan 2018 06:15:27 GMT )
Jan 20, 2018 06:15 UTC
  • An Gargadi Kasar Italia Kan Ta Guji Kawo Sojojinta Cikin Kasar Libya

Wani dan majalisar dokokin kasar Libya mai mazauni a Tabruq ya gargadi kasar Italia kan ta gujewa duk wani kokari na kawo sojojinta cikin kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran Spotnik ya nakalto Ibrahim Addursi yana cewa shigo da sojojin kasar Italia cikin kasar Libya ba abin amincewa ne ga majalisar dokokin kasar ba, kuma mutanen kasar ma ba za su amince da hakan ba. Banda haka suna ganin yin hakan shishigi ne cikin lamuran cikin gida na kasar sannan wani kokari ne na mamayar kasar.

A ranar laraban da ta gabata ce majalisar dokokin kasar Italia ta amince da tura sojojinta 470 zuwa jamhuriyar Niger, sannan zata kara yawan sojojinta a kasar Libya zuwa 400. 

Banda haka Ibrahim Addursi ya suki Gassan Salami jakadan majalisar dinkin duniya na musamman kan jawabin da ya yi  a Majalisar dangane da zaman lafiya a kasar Libya, inda Adduesi yace gabacin kasar Libya bata fama da matsalolin tsaro kamar yadda bangaren yammacin kasar ke fama da shi.