An Zargi Nato Da Aikata Laifukan Yaki A Kasar Libya
(last modified Sat, 20 Jan 2018 19:02:03 GMT )
Jan 20, 2018 19:02 UTC
  • An Zargi Nato Da Aikata Laifukan Yaki A Kasar Libya

Wani lauyan kasar Libya Khalid al-Khuwailady ya kafa kungiyar masana sharia domin tabbatar da laifukan da kungiyar ta Nato ta tafka a kasar Libya

al-Khuwailadi ya kara da cewa; Da akwai kwararan dalilai da su ka tabbatar da cewa A 2011 Nato tana da hannu a laifukan yakin da aka tafka akan fararen hula.

 John Vermon wanda lauya ne na kasa da kasa, kuma mai sa-ido akan kungiyar masu bada kariya ga wadanda hare-haren Nato suka cutar da su a kasar Libya, ya ce; Da akwai wasu hujjojin akan laifin yakin da Nato ta tafka.

A cikin bayanin da Vermon ya fitar a birnin  Brussels da a ciki ya bayyana cewa; Ba da jimawa ba masu bada kariya ga mutanen da harin Nato ya cutar za su gudanar da taron manema labaru.