Jan 27, 2018 05:45 UTC
  • Jamhuriyar Niger Ta Bayyana Rashin Amincewarta Da Shirin Tura Sojojin Italiya Cikin Kasarta

Mahukunta a Jamhuriyar Niger sun bayyana rashin amincewarsu da shirin gwamnatin Italiya na tura sojojinta zuwa cikin kasarsu.

Gidan radiyon Faransa na kasa da kasa ya watsa rahoton cewa: Mahukuntan Jamhuriyar Niger sun sanar da cewa: Babu wanda ya tuntube su kan shirin gwamnatin Italiya na tura sojojin kasarta zuwa cikin kasar Niger, kamar yadda babu wani zaman tattaunawa da aka gudanar a tsakanin mahukuntan kasashen biyu kan wannan batu a baya.

A nashi bangaren fira ministan kasar ta Italiya Paolo Gentiloni ya yi da'awar cewa: Shirin gwamnatin kasarsa na tura sojojinta zuwa Jamhuriyar Niger ya zo ne bayan bukatar da mahukuntan Niger suka gabatar mata.

Tun a ranar 17 ga wannan wata na Janairu ne Majalisar Dokokin Kasar Italiya ta kada kuri'ar amincewa da shirin gwamnatin kasar na kara yawan sojojinta a kasar Libiya tare da tura wasu sojojin kasar 470 zuwa Jamhuriyar Niger da nufin taimakawa a fagen dakile fataucin bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai da kuma yaki da ayyukan ta'addanci da suke ci gaba da addabar kasar.  

Tags